Kanwar Miji Ta Je Har Gida Ta Lakadawa Matar Yayanta Dukan Tsiya, An Gurfanar Da Ita

Kanwar Miji Ta Je Har Gida Ta Lakadawa Matar Yayanta Dukan Tsiya, An Gurfanar Da Ita

  • Yan sanda sun gurfanar da Oluchi Mbadugha a gaban wata kotun majistare da ke yankin Ogba ta jihar Lagas
  • Mbadugha mai shekaru 29 ta yi tattaki har zuwa gidan dan uwanta inda ta yiwa matarsa, Christian Precious, dukan kawo wuka
  • Yanzu haka leben Precious na nan ya yi suntum inda ta samu shaida na dindin bayan fasa mata baki da kanwar mijin tata ta yi

Lagos - An gurfanar da wata mata mai suna Oluchi Mbadugha mai shekaru 29 a gaban kotun Majistare da ke Ogba, jihar Lagas, kan zargin zane matar dan uwanta, Christian Precious.

A cewar takardar kara da yan sanda suka shigar, Oluchi ta ci zarafin matar dan uwanta, Precious, a gidansu da ke yankin Dopemu na jihar Lagas a ranar 12 ga watan Mayu, Shafin LIB ta rahoto.

Kara karanta wannan

Sanata Ekweremadu ya ga ta kan shi a Kotu, an hana shi beli, Alkali ya saki Mai dakinsa

Sandar kotu
Kanwar Miji Ta Je Har Gida Ta Lakadawa Matar Yayanta Dukan Tsiya, An Gurfanar Da Ita Hoto: Thisdaylive
Asali: UGC

Takardar tuhumar ta ce:

“Cewa ke, Oluchi Mbadugha, a ranar 12 ga watan Mayun 2022 da misalin karfe 9:30am a jerin gidajen Sunday Farm, Dopemu Agege, a jihar Lagas, kin aikata laifi na jiwa wata Christian Precious rauni ta hanyar yanka mata leben kasa da kuma haddasa mata tabon rauni na dindindin.”

DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka

Yar sanda mai gabatar da kara, Josephine Ikhayere, ta ce hukuncin laifin na a karkashin sashi na 246(a) na dokar aikata laifi ta jihar Lagas 2015.

Lauyan da ke kare wacce ake tuhuma, Elona Ezulu, shi ne ya jagoranci jami’in ‘yan sanda masu bincike, Insifekta Agbo Blessing, a kan shaida.

Jami’in ya bayyana cewa wacce ke kara ta zo ofishin yan sanda cikin jini da fasasshen lebe.

An dage sauraron shari’ar zuwa 20 ga watan Satumba 2022 don yanke hukunci.

Kara karanta wannan

Yanzu Yanzu: EFCC Ta Gurfanar Da Dakataccen Akanta Janar Na Tarayya A Gaban Kotu Kan Zambar N109bn

Ta Bi Shawarar Kawarta Ta Rabu Da Saurayinta Kan Cewa Ya Cika Girman Kai, Yanzu Kawar Na soyayya Da Shi

A wani labarin, wata matashiyar ‘yan Najeriya mai suna Ugochi ta hadu da cin amana mafi muni bayan kawarta ta fara soyayya da saurayinta.

Tun farko dai kawar Ugochi din ita ta shawarceta da ta rabu da saurayin nata domin a cewarta ya cika takama da izza. Ita kuma sai ta bi shawarar wajen rabuwa da shi.

Ugochi ta je shafinta na Twitter don bayar da labarin wannan cin amana mafi girma da aka yi mata.

Asali: Legit.ng

Online view pixel