Bayan Shekaru 15, Ma’aikacin Banki Ya Nemi Mai Gyaran Takalmin Da Ya Taimakesa, Ya Bashi Tukwici

Bayan Shekaru 15, Ma’aikacin Banki Ya Nemi Mai Gyaran Takalmin Da Ya Taimakesa, Ya Bashi Tukwici

  • Shekaru 15 baya, wani matashin yaro mai suna Edward Asare na a hanyar zuwa makaranta sai takalminsa ya lalace a hanya
  • Wani mai gyaran takalmi gurgu ya taimaka masa wajen gyarawa, amma Asare bai taba mantawa da wannan karamci da mutumin ya yi masa ba duk da dadewarsa
  • Ya koma shagon mutumin don gode masa a 2022, sannan ya je shafin yanar gizo ya bayar da labarin mutumin inda aka samu wani ya gina masa shago

Wani mutum ya ci ribar aikin al’khairin da ya taba yiwa wani matashi dan makaranta shekaru 15 da suka wuce a 2022.

Ma’aikacin banki dan kasar Ghana, Edward Asare ya bayyana yadda wani mai gyaran takalmi gurgu ya taimaka wajen gyara masa takalmin makarantarsa da ya baci a 2007.

Edward Asare
Bayan Shekaru 15, Ma’aikacin Banki Ya Nemi Mai Gyaran Takalmin Da Ya Taimakesa, Ya Bashi Tukwici Hoto: LinkedIn/Edward Asare.
Asali: UGC

An saka masa da alkhairin da ya yi

Kara karanta wannan

Bana karbar canji, manyan kudi nake so: Bidiyon 'dan sanda mai karbar cin hanci babu tsoro

A cewar Asare, yana a hanyarsa ta zuwa makaranta a wata rana kawai sai takalminsa ya lalace.

DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka

Ya ce sai wannan mai gyaran takalmin mai suna Ernest Adu Ansah ya taimaka ya gyara masa takalmin a kyauta ba tare da ya karbi kudi ba.

Asare ya rubuta a shafin LinkedIn:

“Wani lokaci yayin da nake zuwa makaranta, sai wannan nakasasshen mutumin wanda ya kasance mai gyaran takalmi ya ganni rike da takalmina daya a hannu, sai ya kira ni sannan ya gyara mun shi. A kyauta ya yi aikin. Bai karbi ko sisi ba a hannuna.”

Mutumin ya ci ribar aikin nasa

Aikin alkhairin da mutumin ya yi ya kaisa da samun shago na kwantena yayin da Asare ya koma don yi masa godiya.

Ya ci gaba da labarin mai dadi:

Kara karanta wannan

Bidiyo: Ɗan dambe ya lakaɗi matashin da ya zungure shi a Twitter kuma ya bi shi har gida su goge raini

“Wannan ya faru ne a tsakanin 2007/2008. Ban taba mantawa da wannan karamcin ba. A kullun yana zuciyata. Na yi wata wallafa a Twitter game da shi sannan wani da ke zaune kusa da inda yake aiki ya fada mani cewa har yanzu yana wajen.
“Na je na ziyarce shi sannan na fada masa yadda karamcin nasa ya taba zuciyata. Bai tuna ni ba saboda abun ya fi shekaru 16 kuma lokacin ina dan karamin yaro ne wanda ya gyarawa takalmi a kyauta. Wani bawan Allah ya yi masa wannan kwantenan don ya dunga aiki a ciki."

Masu amfani da shafin LinkedIn sun yi martani

Stanley Asamoah Larbi ya ce:

“Na san shi sosai. Ya kasance mutum mai jin kai. A zamani da nake De Youngster's a 1999. Allah ya albarkace shi.”

Belinda Kamasah ta ce:

“Duk yadda kake kallon kankantar abu, yana iya dawowa don taimakonmu a gaba. Za ka girbi abun da ka shuka a lokacin da baka yi tsammani ba. Allah ya albarkace shi. Bai ma tunaka bna amma kai ka yi. Alkhairin da ka yiwa mutane yana tare da su.”

Kara karanta wannan

‘Ya Da Uwa Sun Fashe Da Kukan Kewar Rabuwa Da Juna A Wajen Liyafar Bikin Diyar, Bidiyon Ya Taba Zukata

Kamfanin Dubai Mai Ma’aikata 61,000 Ta Karrama Dan Najeriya A Matsayin Gwarzon Wata

A wani labarin, Yan Najeriya sun jinjinawa wani matashi, Adetunji Olusola Ajao Philip, kan daukaka sunan kasar a Dubai bayan wata karramawar da ya samu a wajen aikinsa.

An karrama Olusola a wajen aikinsa, Transguard Group, a matsayin gwarzon ma’aikaci na watan Yunin 2022.

Wani da ya san matashin da aka karrama, Hajj-Saheed Omo-Iya Kunmi wanda ya wallafa labarin a Facebook ya ce Olusola ya samu lambar yabon ne a babban ofishin kamfanin a ranar Talata, 12 ga watan Yuli.

Asali: Legit.ng

Online view pixel