Ku Hana Su 'Yan Matanku Fitar Da Tsiraici Ranar Aurenku, Fasto Ya Shawarci Amaren Da Zasu Shiga Daga Ciki

Ku Hana Su 'Yan Matanku Fitar Da Tsiraici Ranar Aurenku, Fasto Ya Shawarci Amaren Da Zasu Shiga Daga Ciki

  • Fasto Agyeman Elvis ya shawarci amaren da ke shirin shiga daga ciki da su bude idanunsu wajen zabar irin shigar da kawayensu za su yi a ranar biki
  • Malamin addinin ya ce wasu na zuwa taron ne da nufin janye hankalin ango don ya koma kansu
  • Elvis ya ce shiga ta boye tsiraici abu ne da ya kamata amare su tilastawa kawayensu yin sa a wannan rana

Shahararren fasto, Agyeman Elvis ya shawarci amaren da ke shirin shiga daga ciki a kan su yi taka-tsan-tsan da irin kawayen da suke zaba a matsayin yan matan amarya.

Fasto Agyemang Elvis a cikin wata wallafa da ya yi a shafinsa na Facebook ya bayyana cewa akwai wasu yan mata da ke nuna tsaraicinsu duk don su ja hankalin ango zuwa kansu.

Kara karanta wannan

Karuwa Ta Sharbe Farjin Takwararta Da Reza Bayan Fada Ya Kaure Tsakaninsu Kan Kwastoma, Ta Shiga Hannu

Sannan ya ce manufar wasu kuma shine kure adaka don kawai su nunawa duniya cewa sun fi amaryar kyau.

Fasto da yan mata
Ku Hana Su 'Yan Matanku Fitar Da Tsiraici Ranar Aurenku, Fasto Ya Shawarci Amaren Da Zasu Shiga Daga Ciki Hoto: Facebook/Pastor Agyemang Elvis, Pinterest
Asali: UGC

Malamin addinin ya kuma shawarci amaren da ke tsara yadda aurensu zai kasance da su lura da irin abubuwar da za su bari ayi a wajen taron sannan su tabbatar da ganin an yi shiga ta boye tsiraici.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Ya rubuta a shafin nasa:

“A ranar aure da baikon ku, ku lura dan wadanda kuka zaba a matsayin yan matan amare don yin rawa a gaba da bayanku. Duk wacce ta yi shiga da bai kamata ba a wannan rana tana nuna tsaraicinta tana da manufa sama da zuwa mara maku baya don kasancewa tare da mijinki. Wasu sun zo ne don tabbatar da cewar sun fi ku kyau da diri. Kuma hanya ce ta aika sakonni ga majinki cewa bai kai ido kasuwa ba. Kuma sai ku ga maza sun zo sun fada soyayya da yan matan amare saboda sun ja hankalinsu a ranar auren da baiko.

Kara karanta wannan

El-Rufai: Buhari Bai Ma San Yan Ta'adda Sun Yi Barazanar Sace Shi Ba, Sai Da Na Sanar Da Shi

“Ku zamo masu wayo! Ku bayar da cikakken bayani game da aure da baikonku. Kada ku yi tunanin kan yadda za a pantama kawai, ku shirya yadda za a yi shiga ta kamala. Ku tuna cewa biki na rana daya ne amma aure muddin rayuwa ne. amma idan mutum ya yi kuskure a ranar biki zai iya shafar auren muddin rayuwa.”

Karuwa Ta Sharbe Farjin Takwararta Da Reza Bayan Fada Ya Kaure Tsakaninsu Kan Kwastoma, Ta Shiga Hannu

A wani labarin, rundunar yan sandan kasar Ghana sun kama wata ‘yar Najeriya da ke karuwanci a yankin Ashanti kan zargin amfani da reza wajen yanke farjin abokiyar sana’arta.

Mai laifin wacce aka bayyana a matsayin magajiya uwar dukkan karuwai a Dichemso Plaza ta kuma yi amfani da rezan wajen yayyaga fuska da cinyoyin matar kan zargin ta kwace mata daduronta, shafin LIB ya rahoto.

An tattaro cewa wacce ake zargin mai suna Bella, ta gargadi takwarar tata mai suna Ruth da ta rabu da wannan mutumin saboda shine babban kwastomanta.

Kara karanta wannan

Hashim Raza: Yadda Cutar Kansa Ta Sauya Wani Matashi Mai Jini A Jika, Hotunansa Za Su Tsuma Zuciyar Kowaye

Asali: Legit.ng

Online view pixel