Manyan Labarai A Yau
Firaministan Ingila, Rishi Sunak, ya aike da muhimmiyar wasiƙa zuwa ga zaɓa ɓen shugaban ƙasan Najeriya, Bola Tinubu, ya ce Ingila ta shirya aiki tare da shi.
Rahotanni sun tabbatar da ƴan ta'addan ISWAP sun sace wasu ma'aikatan jinƙai da jami'an tsaro a jihar Borno. Ƴan ta'addan sun lallaɓa cikin dare suka tafi da su
Babbar kotun tarayya mai zaman ta a jihar Legas, ta zartar da hukuncin fatali da umurnin kwace kadarori 14 na gwamnan jihar Kogi, Yahaya Bello, da aka ba EFCC.
Sanata Uzor Orji Kalu ya ziyarci zaɓaɓben shugaban ƙasa, Asiwaju Bola Ahmed Tinubu, a birnin Abuja. Tattaunawar su ba ta rasa dangantaka da kujerar majalisa
Wasu manyan sakatarori guda 6 sun yi rantsuwar kama aiki. Shugaban ƙasa Muhammadu Buhari, shine ya jagoranci rantsar da sabbin sakatarorin domin fara aiki.
Masu garkuwa da mutane sun kai wani mummunan sumame a ƙauyen Yewuti cikin ƙaramar hukumar Kwali ta birnin tarayya Abuja. Sun yi awon gaba da mutane da dama.
Rahotanni sun tabbatar da aukuwar wani mummunan haɗarin mota wanda ya yi sanadiyyar rasuwar wasu jami'an ƴan sanda mutum uku a ƙaramar hukumar Giwa ta Kaduna.
Gwamnatin jihar Benue ba ta son a gudanar da ƙidayar bana cikin wata mai kamawa na Mayu. Gwamnatin ta kawo dalilanta na rashin son an yi ƙidayar da ta ke yi.
Ajeibe Issa, malamin Jami'ar Jihar Kwara, da ke Melete, ya riga mu gidan gaskiya. Rahotanni sun bayyana cewa ya rasu ne a cikin barcinsa kuma an yi jana'izarsa.
Manyan Labarai A Yau
Samu kari