Malamin Jami'ar Najeriya A Jihar Arewa Ya Rasu Yana Cikin Barci

Malamin Jami'ar Najeriya A Jihar Arewa Ya Rasu Yana Cikin Barci

  • Wani malamin jami'ar Kwara ya mutu bayan da ya zarce daga barci a gidansa da ke Ilorin
  • An shirya Jana'iza kamar yadda tsarin addinin musulunci ya tanadar a Budo-Egba da ke karamar hukumar Asa a jihar
  • Hukumar jami'ar ta aike da sakon ta'aziyya ga iyalai, abokai da al'ummar jami'ar kan rasuwar malamin da aka bayyana a matsayin mai kwazo

Jihar Kwara - Wani malami a Jami'ar Jihar Kwara, da ke Melete, Dakta Ajeibe Issa, ya mutu lokacin da yake barci a gidansa da ke Ilorin, babban birnin Jihar Kwara, da safiyar Litinin, The Punch ta rahoto.

Har zuwa rasuwarsa, Yakub shi ne shugaban sashen koyar da lafiyar dan adam da ilimin kiwon lafiya na cibiyar sannan kuma ya kasance daraktan wasanni na riko.

Kara karanta wannan

Hawaye Sun Kwaranya, Allah Ya Yi Wa Fitaccen Alƙalin Babbar Kotun Arewa Rasuwa

Jami'ar Kwara
Malamin Jami'ar Najeriya A Kwara Ya Rasu Yana Cikin Barci. Hoto: The Punch
Asali: Facebook

An ruwaito cewa ana shirye shiryen binne shi kamar yadda addinin musulunci ya tanada a Budo-Egba, karamar hukumar Asa, Jihar Kwara.

Sallee ya ce:

DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka

"Cikin jimami, muna sanar da mutuwar shugaban tsangayar motsa jiki da kiwon lafiya kuma daraktan wasanni na Jami'ar Jihar Kwara, Dakta Ajeiigbe Issa Yaqub.
"Za ayi jana'iza da misalin karfe 10:00 na safiyar yau 24 ga Afrilu, 2023, a Budo-Egba, da ke karamar hukumar Asa ta Jihar Kwara.
"Yayin da jami'ar ke jimamin rashin daya daga cikin ma'aikanta masu kwazo, muna rokon Allah ya yafe kura kurensa ya kuma sanya shi a Jannatul Firdaus.
"Allah ya ba wa iyalansa hakuri, da abokansa da al'ummar jami'ar gaba daya.''

Wani Mutum Ya Gamu Da Ajalinsa A Hanyarsa Ta Dawowa Daga Masallacin Idi A Kwara

A wani rahoto kun ji cewa wani lamari mara dadi ya faru a garin Ilorin, Jihar Kwara a ranar Juma'a a yayin da wani mutum mai matsakaicin shekaru ya rasu sakamakon hadarin mota a ranar Idi.

Kara karanta wannan

Mutum 5 Sun Rasu A Hadarin Jirgin Ruwa A Kano, An Ceto Wasu Shida Da Ransu

Hatsarin ya faru ne a lokacin da Suraju ke kan babur tare da wasu mutane kuma suna dawowa daga sallar Idi kamar yadda The Punch ta rahoto.

A cewar City Round Suraju ya ce ga garin ku ne bayan an garzaya da shi wani asibiti domin a masa magani yayin da sauran mutanen da ke kan babur tare da shi suna karbar magani.

Asali: Legit.ng

Online view pixel