Kotu Ta Yi Fatali Da Neman Belin Da Tukur Mamu Yake Yi a Gabanta

Kotu Ta Yi Fatali Da Neman Belin Da Tukur Mamu Yake Yi a Gabanta

  • Buƙatar Tukur Mamu ta samun beli daga wajen babbar kotun tarayya a Abuja, ba ta cika ba
  • Babbar kotun ta yi fatali da neman belin da Tukur Mamu, ya ke yi a gaban ta kan wasu dalilai
  • Kotun tace Mamu bai kawo cikakkun hujjojin da za su sanya ta bayar da belin sa kamar yadda ya buƙata

Abuja - Wata babbar kotun tarayya mai zaman ta a birnin tarayya Abuja, ta yi fatali da neman belin da Tukur Mohammed Mamu, ya yi a gaban ta.

The Nation tace a wani hukunci da alƙalin kotun, Inyang Ekwo, ya yanke a ranar Alhamis, ya ce ƙorafin da Mamu ya shigar bai samar da cikakkun hujjojin da kotu za ta yi hukuncin da zai masa daɗi ba.

Kotu ta hana belin Tukur Mamu
Ana zargin Tukur Mamu da laifuka da dama Hoto: Thenation.com
Asali: UGC

Mai shari'a Ekwo, ya yi nuni da cewa wanda ake ƙarar ya kasa kare kansa daga zargin da ake cewa akwai yiwuwar zai iya ƙara aikata wasu laifukan da dama, cewar rahoton Channels tv.

Kara karanta wannan

EFCC Vs Gwamna: Babbar Kotun Tarayya Ta Yanke Hukunci Kan Kwace Kadarorin Gwamnan Jihar Arewa

Alƙalin ya ce duk da dai wanda ake ƙarar ya ce hukumar ƴan sandan farin kaya (DSS), inda ake riƙe da shi, ta kasa samar masa da ababen kula da lafiyar sa, kotun sai ta yi la'akari da wasu abubuwan kafin ta yanke hukunci.

DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar

"Kotu za ta yi la'akari da halayyar wanda ake ƙara/mai neman beli, kan kayan duba lafiyar sa da masu tsare da shi suka samar masa." A cewarsa.
"Idan akwai abun duba lafiya a wajen ma su tsare da shi, wanda zai ba yar da cikakkiyar kulawa ga lafiyar wanda ake ƙara, kotu ba za ta saurari neman beli ba kan dalilin rashin lafiya."

Ana tuhumar Mamu da laifuka da dama

A ranar 21 ga watan Maris, 2023 nw dai gwamnatin tarayya ta gurfanar da Tukur Mamu, kan tuhumomi guda 10 na zargin ɗaukar nauyin ta'addanci da sauran su.

Kara karanta wannan

Gwamnatin Tarayya Ta Kashe Naira Miliyan 560 Wajen Ceto ‘Yan Najeriya a Kasar Sudan

An cafke Mamu ne a ranar 7 ga watan Satumban 2022, a filin jirgin sama na Cairo International Airport, kan zargin ɗaukar nauyin ta'addancin Boko Haram.

Peter Obi Ya Ankarar da Kotu a Kan Babbar Hujjar da ke Fallasa 'Magudin' Bola Tinubu

A wani rahoton na daban, Peter Obi ya kawo wata babbar hujja a gaban kotu, domin nuna yadda aka yi wa Bola Tinubu, maguɗi a zaɓen shugaban ƙasa na 2023.

Peter Obi yana son sai lallai an kwace nasarar da Bola Tinubu ya samu a zaɓen 2023.

Asali: Legit.ng

Online view pixel