Bayin Allah Da Dama Sun Jikkata, Dukiyoyi Sun Salwanta a Wani Mummunan Fada Da Ya Barke a Jihar Arewa

Bayin Allah Da Dama Sun Jikkata, Dukiyoyi Sun Salwanta a Wani Mummunan Fada Da Ya Barke a Jihar Arewa

  • Wani mummunan rikici ya ɓarke a garin Doko cikin ƙaramar hukumar Lavun ta jihar Niger
  • Rikicin ya ɓarke ne a tsakanin wasu ɓangarori guda biyu waɗanda ba sa ga maciji da juna a yankin
  • Ba a samu asarar rai ba amma mutane da dama sun jikkata, yayin da aka tafka asarar dukiya mai tarin yawa

Jihar Niger - Kimanin mutum 10 ne suka samu raunika, yayin da kuma aka ƙona wani gida da kayan amfanin gona na miliyoyin naira, a lokacin wani rikici da ya ɓarke a jihar Niger.

Jaridar Daily Trust ta tattaro cewa rikicin ya auku ne a tsakanin wasu ɓangarori biyu masu gaba da juna a garin Doko cikin ƙaramar hukumar Lavun ta jihar Niger

Mutane da dama sun jikkata a rikicin jihar Niger
Taswirar jihar Niger Hoto: Channelstv.com
Asali: UGC

Mazauna garin sun bayyana cewa faɗan ya ɓarke a dalilin fili sannan ya sake dawowa sabo a yammacin ranar Talata bayan tsawon shekaru ya ƙi ci ya ƙi cinyewa.

Kara karanta wannan

Da Dumi-Dumi: Jiragen Yakin Rundunar Soji Sun Yi Taho Mu Gama a Sararin Samaniya, Rayuka Sun Salwanta

An garzaya da mutanen da suka samu raunika zuwa babban asibitiin gwamnatin tarayya, da ke Bida domin duba lafiyar su.

DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka

Da aka tuntuɓe shi, kakakin rundunar ƴan sandan jihar, DSP Wasiu Abiodu, ya tabbatar da aukuwar lamarin.

Ya bayyana cewa aƙalla mutum 6 suka raunata a lokacin faɗan sannan an lalata kayayyaki masu amfani.

"Sai dai, rundunar ƴan sandan nan da nan ta tura jami'an ta zuwa wajen da lamarin ya auku, inda ta cafke mutum 19 da ake zargi da hannun su a cikin rikicin." A cewarsa.

Mazauna garin sun yi kira ga gwamnatin jihar da ta hanzarta sa baki cikin lamarin, kan rikicin filayen da ya daɗe yana aukuwa a yankin, domin cigaba da noma cikin kwanciyar hankali, musamman da yanzu damina ta fara.

Yan Bindiga Sun Kashe Bayin Allah 15 Da Sojoji 2 a Jihar Benue

Kara karanta wannan

Da Ɗumi-Ɗumi: An Tsinci Gawar Ɗan Takarar Gwamna a Zaben 2023 da Aka Kammala

A wani rahoton na daban kuma, kun ji cewa an halaka bayin Allah da dama da wasu sojoji 2, a wani mummunan harin ƴan bindiga a jihar Benue.

Miyagun ƴan bindigan sun kai munanan hare-haren ne a garuruwa uku na cikin ƙaramar hukumar Apa ta jihar. Rayukan farar hula mutum 15 ne aka rasa a yayin harin.

Asali: Legit.ng

Online view pixel