Sanata Uzor Kalu Ya Sanya Labule Da Bola Tinubu a Abuja

Sanata Uzor Kalu Ya Sanya Labule Da Bola Tinubu a Abuja

  • Sanata Uzor Orji Kalu, ya keɓe da zaɓaɓɓen shugaban ƙasa, Bola Tinubu a gidan sa da ke Abuja
  • Sanata Kalu ya sanya labule da Tinubu ne bayan ya dawo gida Najeriya daga hutun da ya je nahiyar turai
  • Kalu yana ɗaya daga cikin masu neman ganin sun ɗare shugabancin kujerar majalisar dattawa ta 10

Abuja - Ɗaya daga cikin masu jan ragamar takarar shugabancin majalisar dattawa, Sanata Orji Uzor Kalu, ya sanya labule da zaɓaɓɓen shugaban ƙasa, Asiwaju Bola Tinubu, ranar Laraba a birnin tarayya Abuja.

Mr Kalu, wanda yanzu haka shine mai tsawatarwa na majalisar dattawa, kafin su sanya labulen, ya nuna godiyar sa ga Allah bisa yadda Tinubu ya dawo gida lafiya daga hutun da ya je, cewar rahoton Premium Times.

Sanata Orji Kalu ya ziyarci Tinubu
Sanata Uzor Kalu tare da Bola Tinubu a Abuja Hoto: @OUKtweets
Source: Twitter

Dalilin zaman na su bai rasa nasaba da takarar neman shugabancin majalisar dattawa ta 10.

Kara karanta wannan

Hadimin Atiku Ya Tono Babban Sirri, Ya Fallasa Yadda Tinubu Ya Shirya Fito Na Fito da Buhari Idan Ya Hau Mulki

Uzor Kalu bayan ganawar sa da Tinubu, ya gayawa ƴan jarida cewa maƙasudin zuwan na sa shine ya yi wa Tinubu barka da zuwa da ta ya shi murnar dawowa daga hutun da ya je nahiyar turai.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Kalu yace ya samu zaɓaɓɓen shugaban ƙasan cikin ƙoshin lafiya, mai cike da jin ƙarfi da kuzari a tattare da shi, cewar rahoton The Cable

A cewar sa, dawowar zaɓaɓɓen shugaban ƙasar cikin ƙoshin lafiya, ya ƙara tabbatar da maganar da ya yi a ranar Juma'a, inda ya yi watsi da maganganun da ake yaɗa wa cewa Tinubu baya da lafiya.

Kalu ya ce ya cancanci zama shugaban majalisar dattawa

A dangane da takarar kujerar majalisar dattawa, Kalu ya ce duk ya fi sauran ƴan takarar cancanta.

A kalamansa:

"Na fi kowa cancanta a cikin ƴan takarar, ina da ƙwarewar da zan iya haɗa kan Najeriya, sannan nine na fi cancanta mu yi aiki tare da zaɓaɓɓen shugaban ƙasar mu domin ciyar da Najeriya gaba."
"Ƴan Najeriya suna buƙatar su ji tasirin jam'iyyar mu. Ina da kirki, gaskiya da ƙwarewar da zan jagoranci majalisar dattawa."

Kara karanta wannan

Karin Bayani: Tinubu Ya Sa Labule da Shugaban APC Na Kasa da Wasu Jiga-Jigai, Bayanai Sun Fito

Betara Ya Ziyarci Tinubu

A wani rahoton kuma, Muktar Betara Aliyu, ya sanya labule da Bola Tinubu a sabon masaukin sa na Defence House, a birnin tarayya Abuja.

Hon. Betara yana daga cikin masu neman kujerar kakakin majalisar wakilai ta tarayya, a majalisa ta 10 wacce za a ƙaddamar a cikin watan Yuni.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal (Hausa Editor) Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng