Majalisa Ta 10: Daga Karshe Tinubu Ya Bayyana Zabin Sa a Shugabancin Majalisar Dattawa

Majalisa Ta 10: Daga Karshe Tinubu Ya Bayyana Zabin Sa a Shugabancin Majalisar Dattawa

  • Ga dukkan alamu rashin tabbas kan waɗanda za su shugabanci majalisar dattawa ta 10 ya zo ƙarshe
  • Zaɓaɓɓen shugaban ƙasa, Bola Tinubu, ya zaɓi Sanata Godswill Akpabio da Sanata Barau Jibrin a matsayin shugabannin majalisar
  • An yi wannan haɗin ne a cewar majiyoyi domin samar da daidaito a madafun ikon ƙasar nan

Abuja - Asiwaju Bola Ahmed Tinubu, ya shirya tsaf domin haɗa tsohon gwamnan jihar Akwa Ibom, Sanata Godswill Akpabio a matsayin shugaban majalisar dattawa da Sanata Barau Jibrin a matsayin mataimakin sa, rahoton Daily Trust ya tabbatar.

Akpabio da Barau suna daga cikin ƴan takara 9 da ke neman shugabancin majalisar dattawa ta 10, wacce ake sa ran za a rantsar da ita a ranar 13 ga watan Yuni.

Tinubu ya bayyana zabin sa a shugabancin majalisar dattawa ta 10
Bola Tinubu da gwamnonin APC a wajen taro Hoto: Bola Tinubu
Asali: Twitter

Majiyoyi masu tushe sun tabbatarwa da Daily Trust cewa, zaɓaɓɓen shugaban ƙasar, ya gayawa Akpabio da Barau wannan hukuncin na sa da ya yanke a yayin wani taro a birnin tarayya Abuja.

Kara karanta wannan

Bayin Allah Da Dama Sun Jikkata, Dukiyoyi Sun Salwanta a Wani Mummunan Fada Da Ya Barke a Jihar Arewa

Tsohon gwamnan na jihar Legas, ya sanya labule a ranar Talata da Akpabio, Barau, Sanata Opeyemi Bamidele da gwamnan jihar Ekiti, Biodun Oyebanji.

DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar

Majiyoyi sun tabbatar da cewa a lokacin ganawar ta su, wacce Tinubu ne ya sanya aka gudanar, an buƙaci Barau da ya janye takarar sa domin samun daidaito, adalci da raba daidai ta fannin addini.

Wani ɗan majalisa daga Kudancin Najeriya, ya ce an shawo kan Barau ya janye takarar sa ne domin daidaituwa da zaman lafiya a ƙasa.

A kalamansa:

"An ce masa ya haƙura da takara domin a samu kirista a matsayin shugaban majalisar dattawa ta 10."
"Bayan an gama roƙon sa ne zaɓaɓɓen shugaban ƙasa ya gayawa Barau cewa yana son ya yi aiki da Akpabio a matsayin mataimakin shugaban majalisar dattawa."

Da ya ke ƙara tabbatar da hakan, wani mamba a kwamitin gudanarwa na ƙasa (NWC) na jam'iyyar APC, ya bayyana cewa Tinubu ya tuntuɓi Akpabio da Barau, akan shawarar da ya yanke na su shugabanci majalisar dattawan.

Kara karanta wannan

Bayan Ganawa da Tinubu, Shugaban APC Ya Yi Magana Kan Wanda Za'a Baiwa Shugabancin Majalisa Ta 10

"Bana wajen lokacin da aka yi taron, amma mutum biyu da suka halarci taron sun gaya min hukuncin da Asiwaju ya yanke. Gaskiya ne ya zaɓi Akpabio da Barau a matsayin shugaba da mataimaki." A cewarsa

Mataimaki Ya Kai Shugaban Jam’iyyar APC Kotu

A wani rahoton na daban kuma, rikicin cikin gida a jam'iyyar APC na ƙara ƙamari, mataimakin shugaban jam'iyya ya maka shugaban jam'iyyar na ƙasa zuwa kotu.

Salihu Lukman ya kai Abdullahi Adamu kotu ne kan wasu zarge-zarge da ya ke masa na yin karan tsaye ga kundin tsarin mulkin jam'iyya.

Asali: Legit.ng

Online view pixel