Gwamnan Jihar Kogi Ya Yi Nasara Kan Hukumar EFCC a Kotu

Gwamnan Jihar Kogi Ya Yi Nasara Kan Hukumar EFCC a Kotu

  • Gwamnan jihar Kogi, Yahaya Adoza Bello, ya samu yin nasara a kotu kan hukumar EFCC
  • Babbar kotun tarayya ta yi fatali da umurnin kwace masa kadarori 14 da hukumar EFCC ta samu a baya
  • Kotun ta ce kundin tsarin mulki ya ba gwamnan kariya, saboda haka EFCC ba ta da hurumin tuhumar sa

Jihar Kogi - Gwamnan jihar Kogi, Yahaya Bello, ya yi nasara kan ƙarar da ya shigar da hukumar hana yaƙi da cin hanci da rashawa ta ƙasa (EFCC), kan ƙwace masa kadarorin sa.

Jaridar Daily Trust ta kawo rahoto cewa, mai shari'a Nicholar Oweibo na babbar kotun tarayya a Legas, ya yi watsi da umurnin kwace kadarori 14 na gwamna Yahaya Bello, da hukumar EFCC ta samu.

Kotu ta hana EFCC kwace kadarorin Yahaya Bello
Gwamnan jihar Kogi, Yahaya Bello Hoto: Vanguard.com
Asali: UGC

Kotun ta kuma yi watsi da ƙarar a bisa dalilin cewa ba ta da hurumin sauraron ta. Alƙalin ya bayyana cewa sashi na 308 na kundin tsarin mulkin Najeriya, ya ba gwamna mai ci ko shugaban ƙasa kariya daga kowace irin tuhuma.

Kara karanta wannan

Peter Obi Ya Ankarar da Kotu a Kan Babbar ‘Hujjar’ da ke Nuna Magudin Bola Tinubu

A ranar 22 ga watan Fabrairu kotun ta bayar da umurnin ƙwacewa na wucin gadi bayan ƙarar da EFCC ta shigar tana neman kwace kadarori 14 da suke a Legas, Abuja da haɗaɗɗiyar daular Larabawa (UAE).

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Sai dai bayan wannan umurnin na kotun, gwamnan ya shigar da ƙarar jayayya da wannan hukuncin na bayar da umurnin ƙwace kadarorin, inda ya nemi da a yi watsi da shi, rahoton Premium Times ya tabbatar.

Gwamnan ya ta'allaƙa ƙarar sa akan cewa kadarorin da aka lissafo, ba na kuɗin haram bane, domin ya mallake su tun kafin ya zama gwamnan jihar Kogi, saboda haka ba ta yadda za ayi ya siye si da kuɗin jihar Kogi.

Ya kuma ƙara da cewa, sashi na 308 na kundin tsarin mulkin Najeriya, an haramta wa EFCC shigar da ƙara akan sa.

Kara karanta wannan

To Fa: Ministan Buhari Ya Faɗi Wanda Zai Iya Hana Rantsar da Tinubu a Matsayin Shugaban Ƙasa

Matawalle Ya Sheka Kotu Kan Zaben Gwamnan Zamfara

A wani rahoton na daban kuma, gwamnan jihar Zamfara, Bello Matawalle, garzaya kotu kan sakamakon zaben gwamnan jihar, wanda ya yi rashin nasara.

Gwamnan ya sha alwashin sai ya kwato nasarar sa da aka tauye masa, a gaban kotu.

Asali: Legit.ng

Online view pixel