Gwamnati Ta Tsaida Ranakun Bude Titunan Kano-Zaria-Kaduna, Legas-Ibadan, da Gadar Neja

Gwamnati Ta Tsaida Ranakun Bude Titunan Kano-Zaria-Kaduna, Legas-Ibadan, da Gadar Neja

  • Nan da tsakiyar watan Mayu, za a iya kaddamar da titin Kano-Zaria da kuma na Zaria-Kaduna
  • Kafin nan, ‘Yan kwangila za su mikawa gwamnatin tarayya hanyar Legas-Ibadan da aka fadada
  • Haka zalika za a bude gadar Neja kafin Muhammadu Buhari ya sauka daga mulki a karshen Mayu

Abuja - Ministan yada labarai da al’adu, Lai Mohammed ya ce ‘yan kwangilan da ke hanyoyin Kano-Zaria da Zaria-Kaduna sun kusa gama aikinsu.

Kamar yadda rahoto ya zo a Daily Trust, Alhaji Lai Mohammed ya ce za mikawa gwamnati wadannan tituna da gadar Neja a ranar 15 ga Mayu.

Mai girma Ministan ya yi wa manema labarai bayanin nan bayan kammala taron majalisar Ministoci na FEC a fadar shugaban kasa da ke Abuja.

Lai ya shaida cewa a ranar 30 ga watan Afrilun nan za a mika masu babban titin Legas-Ibadan mai tsawon kilomita 116 da gwamnatinsu ta fadada.

Kara karanta wannan

Jirgin saman NigeriaAir Zai Fara Tashi Kafin Shugaba Buhari Ya Bar Aso Rock – Minista

Gadar Neja ta ci Biliyoyi

A kwangilar gadar Neja ta biyu, rahoton ya nuna an kara N1.398bn a kudin kwangilar a dalilin karasa aikin wani bangare na gadar Uto a jihar Delta.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Gadar mai tsawon kilomita 2.6 da ta ratsa garin Ikenke ta jawo kudin kwangilar da gwamnatin tarayya ta biya ya karu daga N4.435bn zuwa N5.835bn.

Titi.
Hanyar Kaduna-Zaria Hoto: @FMWHNIG
Asali: Twitter

Wasu ayyuka da aka karasa

Ministan ya ce an gama gadar Loko-Oweto, haka zalika gadar Ikom da sakatariyoyin gwamnatin tarayya da ke Nasarawa, Awka, Bayelsa da Zamfara.

Komai ya kammala wajen gina gidaje 700 a Zuba, abin da ya rage shi ne a kaddamar da su.

Sun ta rahoto Ministan labaran kasar yana mai farin cikin bada sanarwar karkare titin Kano-Zariya mai 137km da Zaria-Kaduna mai tsawon 73km.

Kara karanta wannan

Gwamnatin Tarayya Ta Kashe Naira Miliyan 560 Wajen Ceto ‘Yan Najeriya a Kasar Sudan

FEC ta amince da kudin wasu ayyuka

A jawabinsa, karamin Ministan ilmi, Goodluck Opiah ya shaida cewa majalisar FEC ta amince a kashe N32.4bna karasa babban dakin karatu na kasa.

Ministan gona ya ce an yi na’am da fara kashe N6bn a gina wani wuri da za a kira gidan noma.

Jibrin a gidan Tinubu

Ku na da labari mutane sun rasa me ya kai zababben ‘dan majalisar mazabar Kiru da Bebeji a Jam’iyyar NNPP, Abdulmumin Jibrin wajen Bola Tinubu.

A takarar 2023, Jibrin yana cikin wadanda suke magana da yawun Rabiu Kwankwaso, kwatsam sai ga shi a gidan shugaba mai jiran gado.

Asali: Legit.ng

Online view pixel