Innalillahi: Mummunan Hadarin Mota Ya Salwantar Da Rayukan 'Yan Sanda 3, Da Dama Sun Jikkata

Innalillahi: Mummunan Hadarin Mota Ya Salwantar Da Rayukan 'Yan Sanda 3, Da Dama Sun Jikkata

  • Wani mummunan haɗarin mota tafi da rayukan wasu jami'an ƴan sanda guda uku a jihar Kaduna
  • Haɗarin a auku ne a cikin wani ƙauye na ƙaramar hukumar Giwa ta jihar yayin da motar ƴan sandan ke tafiya
  • Tayar motar ƴan sandan ce dai ta fashe mu su suna tsaka da tafiya a kan hanyar su ta koma wa bakin aikin su

Jihar Kaduna - Wani mummunan haɗarin mota ya janyo asarar rayukan wasu jami'an ƴan sanda mutum uku a jihar Kaduna.

Mummunan haɗarin ya auku na a wajen ƙauyen Kidandan cikin ƙaramar hukumar Giwa ta jihar, rahoton jaridar Daily Trust ya tabbatar.

'Yan sanda uku sun halaka a hadarin mota a Kaduna
Taswirar jihar Kaduna Hoto: Punch.com
Source: UGC

Ƴan sandan suna kan hanyar su ne ta komawa ƙaramar hukumar Giwa, bayan sun halarci hawan Daushe a ci gaba da shagulgulan murnar ƙaramar Sallah a birnin Zazzau, da misalin ƙarfe 9 na dare.

Kara karanta wannan

Ana Dab Da Fara Kidaya, Gwamnatin Jihar Arewa Ta Yi Kiran a Dakata, Ta Kawo Dalilanta

Yadda haɗarin ya auku

Ɗaya daga cikin tayar motar ƴan sandan ne ta fashe a ƙauyen Sako cikin mazaɓar Kidandan, wanda hakan ya yi sanadiyyar rasa rayukan ƴan sanda uku.

DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar

Majiyoyi sun tabbatar da cewa an garzaya da wasu jami'an ƴan sandan uku zuwa asibiti saboda raunikan da suka samu domin a ba su magani, cewar rahoton Independent

Wasu hotuna marasa kyan gani sun nuna jami'an ƴan sandan kwance male-male cikin jini inda wasu daga ciki suka samu munanan raunika a kawunan su

Kakakin rundunar ƴan sandan jihar Kaduna, DSP Mohammed Jalige, ya tabbatar da aukuwar haɗarin, ina ya yi addu'a ga waɗanda suka riga mu gidan gaskiya sannan ya yi wa waɗanda suka samu raunika fatan samun waraka cikin ƙanƙanin lokaci.

Gwamnatin Jihar Benue Ta Yi Kiran Da a Dakatar Da Kidayar 2023

A wani rahoton na daban kuma, kun ji yadda gwamnatin jihar Benue, ta yi kiran da a dakatar da ƙidayar da aka shirya gudanarwa a cikin wannan watan na Mayu.

Gwamnatin jihar tace kamata yayi a ɗage gudanar da ƙidayar har sai mutanen da aka raba da matsugun nan su, sun koma gidajen su, inda ta yi nuni da cewa ba mutane kaɗai ake ƙidaya wa ba har da gidajen su.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal (Hausa Editor) Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng