Firaministan Ingila Ya Rubuto Wata Muhimmiyar Wasika Ga Tinubu

Firaministan Ingila Ya Rubuto Wata Muhimmiyar Wasika Ga Tinubu

  • Firaministan Ingila ya rubuto wata wasiƙa ta musamman zuwa ga zaɓaɓɓen shugaban ƙasa Bola Tinubu
  • Rishi Sunak ya bayar da tabbacin son yin aiki kafaɗa da kafaɗa da zaɓaɓɓen shugaban ƙasan na Najeriya
  • Rishi ya ce Ingila a shirye ta ke ta cigaba da ƙara ƙarfafa dangantakar da ke a tsakanin ƙasashen biyu

Abuja - Firaministan United Kingdom (UK), Rishi Sunak, ya rubuto wata takarda ta musamman zuwa ga zaɓaɓɓen shugaban ƙasa, Bola Tinubu, kafin zuwan ranar rantsar da shi kan karagar mulki.

A wata wasiƙa da jaridar The Cable ta ci karo da ita, Sunak ya bayyana cewa a shirye ya ke ya yi aiki kafaɗa da kafaɗa da Tinubu, wanda ya lashe zaɓen shugaban ƙasa a ƙarƙashin inuwar jam'iyyar All Progressives Congress (APC), a watan Fabrairu.

Kara karanta wannan

Da Dumi-Dumi: Mai Neman Shugabancin Majalisar Wakilai Ya Shiga Kus-Kus Da Tinubu, Bayanai Sun Bayyana

Rishi Sunak Ya Rubuto Wasika Ga Tinubu
Firaministan Ingila, Rishi Sunak Hoto: Rishi Sunak
Asali: Facebook

Sunak ya bayyana cewa yana fatan ya tarbi Tinubu a birnin Landan a watan Afirilun 2024, a wajen taron zuba jari a nahiyar Afirika kashi na biyu.

"Taron zai kasance wani lokaci mai muhimmanci domin ƙara ƙarfafa dangantakar kasuwancin Najeriya da UK, domin samar da ayyukan yi da cigaba, ƙara zuba jari a ƙasashen biyu da kasuwanci da kuma taimaka masa wajen ɓunƙasa ƙarfin fitar da kaya zuwa ƙasashen waje." A cewarsa.

DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar

"A tare za mu iya ƙara ƙarfafa dangantakar mu, ta hanyar ƙarfafa alaƙar kasuwanci da zuba jarin mu, domin amfanin ƙasashen mu gabaɗaya, ta hanyar ƙara ƙarfin danƙon kasuwanci da zuba jari."

The Cable tace firaministan ya ce UK za ta cigaba da taimaka wa Najeriya wajen magance matsalar tsaron ta, ta hanyar ba ta horarwa da kayan aiki.

Wani ɓangare na wasiƙar ya cigaba da cewa:

Kara karanta wannan

Kuma Dai: An Shigar Da Wata Sabuwar Karar Neman a Hana Rantsar Da Tinubu a Matsayin Magajin Shugaba Buhari

"Ina fatan za mu cigaba da aikin mu wajen shawo matsalar tsaron da ke fuskantar Najeriya da sauran yankin. Waɗannan ƙalubalen ba sun tsaya ba ne kawai a iyakokin ƙasa, yana da muhimmanci mu cigaba da musanyar horarwa da kayan aiki domin magance su."
"Mai bayar da shawara kan harkokin tsaro ka ƙasa ya shirya domin tattaunawa da mai bayar da shawara kan harkokin tsaro na ƙasar ka, nan gaba a cikin wannan shekarar."
"Danƙon zumuncin da ya ke tsakanin ƙasashen mu biyu ba kawai ya samu ba ne daga alaƙa mai ƙarfi da ke a tsakanin al'ummar mu, ta hanyar ilmi, zane-zane da wasanni, amma da kuma ta hanyar alaƙar mu da ke a ƙasashe rainon Ingila."

Sunak ya kuma ƙara da cewa zai cigaba da tattaunawa da Tinubu da ƴan tawagar sa, a cikin wannan lokacin na miƙa mulki har ya zuwa lokacin rantsuwa.

Shugaba Zelensky Ya Taya Bola Tinubu Murnar Lashe Zabe, Ya Gayyace Shi Zuwa Ukraine

Kara karanta wannan

Bayanai Sun Fito Daga Tsagin Atiku, Da Yuwuwar Ba Za'a Rantsar da Tinubu a Matsayin Shugaban Ƙasa Ba

A wani rahoton na daban kuma, shugaban ƙasar Ukraine ya taya Bola Tinubu murnar zama zaɓaɓɓen shugaban ƙasan Najeriya.

Volodomyr Zelensky ya kuma gayyaci Tinubu ya kawo ziyara zuwa ƙasar Ukraine.

Asali: Legit.ng

Online view pixel