Manyan Labarai A Yau
Shugaban jam'iyyar All Progressives Congress (APC) na ƙasa, Abdullahi Umar Ganduje ya magantu kan yadda jam'iyyar za ta lashe zaɓen gwamnan jihar Bayelsa.
Abba Kabir Yusuf ya amince da karin nadin mukamai 116 a gwamnatinsa. Abba Gida Gida ya bada mukaman SSA, masu ba shi shawara da masu taimaka masa.
Kwamitin amintattu (BoT) na jam’iyyar New Nigeria Peoples Party (NNPP) ta amince da korar Sanata Rabiu Musa Kwankwaso, dan takararta na shugaban kasa a zaben 2023.
Kotun sauraron kararrakin zabe a jihar Delta ta yi watsi da karar da jam’iyyar APC da Sanata Ovie Omo-Agege suka shigar kan nasarar Gwamna Sheriff Oborevwori.
Wata matashiyar budurwa yar Najeriya ta haddasa cece-kuce bayan bayyanan hotunanta tare da masoyinta dan tsurut. Ta daga shi sai kace dan karamin yaro.
Kotun sauraron kararrakin zaben gwamnan jihar Kaduna, ta tabbatar da Gwamna Uba Sani na jam’iyyar All Progressives Congress (APC) a matsayin wanda ya lashe zabe.
Ƙungiyar ƙwadago ta musanta batun cewa ta cimma yarjejeniya da gwamnatin tarayya domin fasa shiga yajin aikin sai baba-ta-gani da take shirin shiga.
Gwamnatin tarayya ta ayyana ranar Litinin, 2 ga watan Oktoba a matsayin ranar hutu domin murnar zagayowar ranar ‘yancin kai. Bikin zai kasance irinsa na biyu.
Ma'aikatan ma'aikatun ayyuka da gidaje sun gudanar da zanga-zanga a Abuja domin nuna adawarsu da salon mulkin ministan ayyuka, Sanata Dave Nweze Umahi.
Manyan Labarai A Yau
Samu kari