Rusau: Gwamnatin Jihar Kano Za Ta Daukaka Kara Kan Hukuncin Kotu Na Biyan Diyyar N30bn

Rusau: Gwamnatin Jihar Kano Za Ta Daukaka Kara Kan Hukuncin Kotu Na Biyan Diyyar N30bn

  • Gwamnatin jihar Kano ta yi martani kan hukuncin kotu na umartarta da ta biya diyyar N30bn ga masu shaguna a filin masallacin Idi
  • Gwamnatin ta hannun kwamishinan shari'a na jihar ta bayyana cewa za ta ɗaukaka ƙara kan hukuncin kotun
  • Kwamishinan ya bayyana cewa gwamnatin tana da dukkanin takardun da ake buƙata domin ƙalubalantar hukuncin a kotun ɗaukaka ƙara

Jihar Kano - Gwamnatin jihar Kano ta mayar da martani kan hukuncin da wata babbar kotun tarayya ta yanke na biyan diyyar Naira biliyan 30 ga masu shaguna a Massallacin Sallar Idi, kan ruguza shagunansu ba bisa ƙa’ida ba, tare da rashin bin ƙa’idojin da doka ta shimfida.

Jaridar Daily Trust ta rahoto cewa mai Shari’a Samuel Amobeda, a ranar Juma'a, 29 ga watan Satumba, a hukuncinsa ya bayyana matakin da gwamnatin ta ɗauka matsayin mugunta wanda ya saɓawa kundin doka.

Kara karanta wannan

Gwamnatin Tinubu Ta Kira Zaman Gaggawa da NLC da TUC a Abuja, Bayanai Sun Fito

Gwamnatin Kano za ta daukaka kara
Gwamnatin jihar Kano ta yi martani kan hukuncin kotu domin biyan diyyar N30bn Hoto: Abba Kabir Yusuf
Asali: Twitter

Idan dai za a iya tunawa, a watan Yuni ne gwamnatin gwamna Abba Kabir Yusuf ta ruguza shagunan da ke kusa da filin Idi na Kano, inda ta bayyana gine-ginen a matsayin haramtattun gine-gine.

Matakin a cewar gwamnatin na daga cikin alƙawuran da ta dauka a yakin neman zabe ga al'ummar jihar Kano.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Sai dai ƴan kasuwar da ke ƙarƙashin ƙungiyar Incorporated Trustees ta masu shagunan a masallacin Idin, sun ƙalubalanci rusau ɗin a babbar kotun tarayya.

Wane mataki gwamnatin Kano za ta ɗauka?

Sai dai, da yake mayar da martani kan hukuncin kotun, kwamishinan shari'a kuma babban lauyan jihar, Haruna Dederi, ya ce hukuncin ba shi da tushe balle makama, kuma gwamnati na da duk wasu takardu da ake buƙata domin ɗaukaka ƙara kan hukuncin.

A kalamansa:

"Za mu ƙalubalanci hukuncin a kotun ɗaukaka ƙara, kuma a bayyane yake dokar amfani da filaye ta fito ƙarara ta nuna ikon da gwamna ke da shi kan filaye a jiha musamman a birane."

Kara karanta wannan

Kungiyar Kwadago Ta Cimma Yarjejeniya Da FG Domin Fasa Shiga Yajin Aiki? Gaskiya Ta Fito

Abba Gida-Gida Ya Yi Sabbin Nade-Nade

A wani labarin kuma, gwamnan jihar Kano Abba Kabir Yusuf wanda aka fi sani da Abba Gida-Gida, ya yi sabbin naɗe-naɗen hadimai a gwamnatinsa.

Gwamnan ya naɗa ƙarin hadimai 116 a gwamnatinsa waɗanda suka haɗa da manyan masu ba da shawara 63, masu bayar da shawara na musamman 41 da hadimai 12.

Asali: Legit.ng

Online view pixel