Alhajin Birni Ya Yi Wa Budurwa Alkawarin Miliyan 3 Da Tafiya Hutu Waje Idan Ta Boye Soyayyarsu

Alhajin Birni Ya Yi Wa Budurwa Alkawarin Miliyan 3 Da Tafiya Hutu Waje Idan Ta Boye Soyayyarsu

  • Wata matashiyar budurwa yar Najeriya ta yada hoton hirarsu da wani alhajin birni a Whatsapp
  • Matar mutumin ta gano alakar da ke tsakaninsu sannan ta gaggauta karbar lambar budurwar mijin nata daga wayarsa
  • Jama'a sun nuna kaduwarsu kan lamarin inda mutane da dama suka caccaki matashiyar kan kulla alaka da magidanci mai aure

Wata matashiyar budurwa yar Najeriya mai suna @lizzywardrobe_and_jewelsn a TikTok ta bayyana abun da ya wakana tsakaninta da wani alhajin birni.

Ta saki hoton wani sako da ta yi ikirarin alhajin nata ya tura mata ta dandalin WhatsApp.

Matashiya ta saki hoton hirarsu da wani alhajin birni
Alhajin Birni Ya Yi Wa Budurwa Alkawarin Miliyan 3 Da Tafiya Hutu Waje Idan Ta Boye Soyayyarsu Hoto: @lizzywardrobeandjewels/TikTok
Asali: TikTok

Sakon na tattare da wasu manyan alkawara na kyaututtuka da hutu da zai kai ta, sannan ya kuma umurceta da ta bayyana kanta a matsayin yar uwarsa idan matarsa ta kirata.

Sai dai kuma, wasu masu amfani da soshiyal midiya sun nuna shakku, suna masu dasa alamar tambaya a kan sahihancin sakon tare da nuna cewa watakila an kirkiri sakon ne.

Kara karanta wannan

An Nadawa Jarumar TikTok Murja Kunya Dukan Kawo Wuka a Kano

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Sakon ya ce:

"Barka masoyiya. Yanzun nan matata ta karbi lambar wayarki daga wayana na yi mata karyar cewa ke yar uwata ce, saboda na yi amfani da sunan "Sisto" wajen ajiye lambarki. Don Allah babi idan ta kira, ki fada mata cewa ni dan uwanki ne.
"Na yi maki alkawarin tafiya hutu zuwa duk kasar da kike so a mako mai zuwa kuma zan aika maki da naira miliyan 3 yanzu don ki yi karyar. Ina fatan kin kawo karshen alakarku da wannan gaulan saurainyin da yake yawan tambayarki 'data' da 2k a kowani lokaci. Ina so ki zama tawa ni kadai. Zaddy na kaunarki."

Matashiya ta yi martani yayin da alhajin birni ya yi mata alkawarin miliyan 3

Da yake martani ga sakon, Lizzy ta yi alkawarin yi wa mabiyanta kyauta idan alhajin nata ya bata naira miliyan 3 da ya yi alkawari.

Kara karanta wannan

“Ba Zai Ci Amana Ba”: Budurwa Yar Najeriya Ta Yi Caraf Da Masoyinta Da Tsurut Kamar Karamin Yaro

Ta rubuta:

"Duk ku ajiye lambar asusunku da zaran zaddyna ya tura miliyan 3 din zan yi maku kyauta."

Jama'a sun yi martani

@thrift_bybella| ta yi martani:

"Da ni da ke mun san cewa karya ce."

@Codedangel ta ce:

"Hasashe zai ji wa wannan ciwo."

@Shima ta yi martani:

“Aaaahhhhh kun cika karya a manhajar nan."

Matashi ya bayyana halin ban tsoro da ya riski kansa bayan ya kwana gidan budurwa

A wani labarin kuma, wani matashi dan Najeriya, @TheOnlyATM, ya haddasa cece-kuce a soshiyal midiya bayan ya bayyana halin da ya shiga a lokacin da ya kwana a gidan wata matashiyar budurwa.

@TheOnlyATM, ya bayyana mummunan yanayin da ya shiga bayan wani shahararre a dandalin X, Agba, ya bukaci maza da su bayyana mummunan abun da ya faru da su a ranar da suka kwana a gidan mace.

Asali: Legit.ng

Online view pixel