Matashi Ya Bayyana Mummunan Yanayin Da Ya Shiga Bayan Ya Kwana a Gidan Budurwa

Matashi Ya Bayyana Mummunan Yanayin Da Ya Shiga Bayan Ya Kwana a Gidan Budurwa

  • Wani matashi dan Najeriya ya bayyana yanayi mai ban tsoro da ya shiga bayan ya zabi kwana a gidan wata matashiyar budurwa
  • Da tsakar dare, matashin ya ce ya yi mummunan mafarki inda wani aljani ya yi kokarin makure shi
  • Bayan ya bude idanunsa, abun da ya gani ya sanya shi fara addu'a neman tsari kafin karfe 4:00 na asuba

Wani matashi dan Najeriya, @TheOnlyATM, ya haddasa cece-kuce a soshiyal midiya bayan ya bayyana halin da ya shiga a lokacin da ya kwana a gidan wata matashiyar budurwa.

@TheOnlyATM, ya bayyana mummunan yanayin da ya shiga bayan wani shahararre a dandalin X, Agba, ya bukaci maza da su bayyana mummunan abun da ya faru da su a ranar da suka kwana a gidan mace.

Kara karanta wannan

“Ba Zai Ci Amana Ba”: Budurwa Yar Najeriya Ta Yi Caraf Da Masoyinta Da Tsurut Kamar Karamin Yaro

Matashi da budurwa a daki
Matashi Ya Bayyana Mummunan Yanayin Da Ya Shiga Bayan Ya Kwana a Gidan Budurwa Hoto: Delmaine Donson. An yi amfani da hoton don misali ne kawai
Asali: Getty Images

Ya yi mummunan mafarki

Matashin ya ce ya yi mummunan mafarki da tsakar dare. A cikin mafarkin, ya ce ya kasa yin ihu domin wani aljani ya yi kokarin makure shi. @TheOnlyATM ya farka sai kawai ya ga matashiyar tana magana da kanta.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Ya tuna cewa kafafunta sun kasance a saman bango yayin da take magana da kanta. Wannan ya tsorata shi. Mai amfani da dandalin na X ya ce:

"Agba, na ziyarci wata matashiyar budurwa a baya don haka na kwana a wajenta. Da tsakar dare, na yi wani mummunan mafarki, kamar wani aljani na kokarin makure ni kuma na kasa ihu. Don haka sai na bude idona kawai sai na ga matashiyar nan ta sakala kafafunta a saman bango sannan tana magana da kanta. Na kusan karar da jinin Yesu kafin karfe 4 na asuba."

Kara karanta wannan

Ana wata ga wata: Wike ya kori manyan jami'an hukumomi da kamfanonin FCTA

Kalli wallafarsa a kasa:

Halin da ya riski kansa ya tsorata mutane

@Unusualsamuel ya ce:

"Mayya ce.
"A bisa al'adar Yarbawa, haka mayu suke tafiya da daddare. Na ji labarin haka amma ban taba fuskantar haka kamar kai ba.
"Hakan na nufin sai ka dage da addu'a duk da cewar ba ku tare da juna saboda mayu basa wasa da sirrinsu."

@enadiose_godwin ya ce:

"Duk mata haka suke yawanci idan ka yi masu laifi, shakka babu za su farka a tsakar dare suna kallonka. A duk lokacin da ni da budurwata muka samu matsala bana kwana da ita a gida daya kuma."

@Alexaxa83210590 ya ce:

"Nina na fuskanci irin haka, na ziyarci wannan budurwar sai na yanke shawarar kwana a can, na farka da misalin karfe 2:00 na tsakar dare sannan na ganta zaune a duhu, idanunta na haskawa kamar mage tana kallona, nagode Allah da rayuwata fa."

Ana ruwa amma ba a dauke wuta ba: Dan Najeriya da ke zaune a Turai ya cika da mamaki

Kara karanta wannan

Masani Ya Hasko Abubuwan Da Za Su Jawo Kayan Abinci Su Yi Masifar Tsada a Najeriya

A wani labari na daban, wani dan Najeriya da ke zaune a Birtaniya ya cika da mamakin dalilin da yasa ba a dauke wutar lantarki ba a yankin da yake duk da ruwan sama mara yankewa da ake ta yi.

Mutumin ya ce an jera tsawon kwana bakwai ana zuba ruwa a yankin da yake, amma ya lura cewa har lokacin akwai wutar lantarki duk da ruwan saman da ake yi.

Asali: Legit.ng

Online view pixel