Kungiyar Kwadago Ta Musanta Cimma Yarjejeniya Da FG Domin Fasa Shiga Yajin Aiki

Kungiyar Kwadago Ta Musanta Cimma Yarjejeniya Da FG Domin Fasa Shiga Yajin Aiki

  • Ƙungiyar ƙwadago ta ƙasa (NLC) ta musanta batun cewa ta cimma yarjejeniya da gwamnatin tarayya domin fasa shiga yajin aiki
  • Ƙungiyar ta ce sam babu jarjejeniyar da ta cimmawa da FG inda ta ƙara da cewa ko ranar tattaunawa domin magance matsalar ba su sanya ba
  • A ranar 3 ga watan Oktoba da ke tafe ne dai ƙungiyar ƙwadagon ta shirya fara yajin aikin sai baba-ta-gani

FCT, Abuja - Ƙungiyar ƙwadago ta ƙasa (NLC) a ranar Alhamis, 28 ga watan Satumba, ta musanta cewa ta cimma yarjejeniya da gwamnatin tarayya domin dakatar da yajin aikin sai baba-ta-gani da ke shirin fara wa daga ranar 3 ga watan Oktoba, cewar rahoton Vanguard.

A ranar Talata ne ƙungiyoyin kwadagon da suka haɗa da NLC da kungiyar ƴan kasuwa ta ƙasa (TUC), suka sanar da cewa ma'aikata za su tafi yajin aikin sai baba-ta-gani, sakamakon gazawar gwamnati na samar da kayan tallafin da za su magance raɗaɗin cire tallafin man fetur.

Kara karanta wannan

Jerin Fastocin Da Suka Yi Hasashen Za a Cafke Peter Obi a Watan Satumba

Kungiyar kwadago ta musanta cimma yarjejeniya da FG
Shugabannin kungiyar kwadago tare da Shugaba Tinubu Hoto: @DOlusegun
Asali: Twitter

Wasu rahotanni sun bayyana cewa daraktan watsa labarai na ma'aikatar kwadago da ayyukan yi, Mista Olajide Oshundun, ya ce akwai yarjejeniya tsakanin kungiyoyin kwadago da gwamnati na dakatar da yajin aikin da ake shirin fara wa.

Ko da yake Oshundun ya musanta cewa ya ce haka, kungiyar ta NLC ta ce babu wata yarjejeniya ko kaɗan kuma gwamnati ba ta gayyaci kungiyar ba, ko sanya ranar tattaunawa da ƙungiyar kan yajin aikin da take shirin yi.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Da gaske NLC ta cimma yarjejeniya da FG?

Tribune ta ce ƙungiyar NLC a cikin wata sanarwa da shugaban watsa labarai da hulɗa da jama’a na ƙungiyar, Benson Upah, ya fitar, ta ce sam ba ta cimma wata yarjejeniya da gwamnayin tarayya kan dakatar da shiga yajin aikin ba.

Wani ɓangare na sanarwar na cewa:.

"Na farko, ba mu da wata yarjejeniya da gwamnati don dakatar da shirin yajin aikin. Haka nan ba mu da wata ranar tattaunawa da gwamnati wacce za ta kai ga dakatar da yajin aikin da ake shirin yi."

Kara karanta wannan

Kungiyoyin Kwadago NLC da TUC Sun Ayyana Shiga Yajin Aikin Sai Baba Ta Gani a Najeriya, Sun Faɗi Rana

“Duk da cewa ba mu da niyyar wulakanta ofishin mai girma ministan kwadago da samar da ayyukan yi, wannan lamari ya ya fi ƙarfin ma'aikatar. Ya kamata ace sun fahimci hakan a taron da muka yi na baya-bayan nan."

An Kulle Ministan Tinubu a Ofis

A wani labarin kuma, ministan ayyuka na ƙasa ya samu saɓani tsakaninsa da ma'aikatan da ke aiki a ma'aiktarsa.

Ma'aikatan sun kulle Dave Umahi a ofis bayan sun zargi ministan da tsaurarawa wajen tafiyar da al'amuran ma'aikatar.

Asali: Legit.ng

Online view pixel