Karin Bayani: Kotun Zabe Ta Yanke Hukunci Kan Zaben Gwamnan Jihar Kaduna

Karin Bayani: Kotun Zabe Ta Yanke Hukunci Kan Zaben Gwamnan Jihar Kaduna

  • Kotun zaben gwamnan jihar Kaduna ta tabbatar da nasarar Gwamna Uba Sanin a jam’iyyar APC a zaben 2023
  • Kotun zaben ta yi fatali da karar da jam’iyyar PDP da dan takararta, Isah Ashiru suka shigar na kalubalantar nasarar Uba Sani
  • Kwamitin kotun zaben karkashin mai shari'a Victor Oviawe ya yanke hukunci ta manhajar Zoom a ranar Alhamis, 28 ga watan Satumba

DUBA NAN: Bibiyi shafin Legit.ng Hausa a kafar TikTok. Kada ka bari bidiyo mai daukar hankali ya wuce ka!

Jihar Kaduna - Kotun sauraron kararrakin zaben gwamnan jihar Kaduna ta tabbatar da nasarar Gwamna Uba Sani, rahoton Daily Trust.

Da yake yanke hukunci kan karar da jam’iyyar Peoples Democratic Party (PDP) da dan takararta, Isah Mohammed Ashiru, suka shigar don kalubalantar nasarar Gwamna Uba Sani, kwamitin kotun ya riki cewa Sani ne zababben gwamna.

Kotun zabe ta tsige Uba Sani daga kujerar gwamnan Kaduna
Kotun Zaben Gwamnan Kaduna Ta Tsige Uba Sani, Ta Ayyana Zaben a Matsayin Ba Kammalalle Ba Hoto: Uba Sani
Asali: Facebook

Hukumar zabe ta kasa mai zaman kanta (INEC) ta ayyana Sani, wanda yay i takara a jam’iyyar All Progressives Congress (APC), a matsayin wanda ya lashe zaben na ranar 18 ga watan Maris.

Kara karanta wannan

"Bamu Yarda Ba" Jam'iyyar PDP Ta Fusata Bayan Kotu Ta Yanke Hukunci Kan Nasarar Gwamnan APC

Ashiru da jam’iyyarsa sun ki amincewa da sakamakon inda suka nufi kotu.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Kwamitin mutum uku karkashin jagorancin mai shari'a Victor Oviawe ya yanke hukunci ta manhajar Zoom ranar Alhamis, 28 ga watan Satumba.

Gwamna Uba Sani ya yi martani kan hukuncin kotun zabe

Uba Sani ya fitar da wata sanarwa a shafinsa na Facebook inda yake tabbatar da nasararsa a kotun zaben.

Ya ce:

"“Na yi matukar farin ciki da kuma kankan da kai ga hukuncin da kotun sauraren kararrakin zabe ta yanke na tabbatar da nasarar da na samu a zaben Gwamnan Jihar Kaduna a 2023.
“Hukuncin ya tabbatar da yawan kuri’un da mutanen jihar Kaduna masu karamci suka bani.
“Na yaba wa kotun kan tsayin dakan da suka nuna. Sun inganta bangaren shari'armu da tsarin dimokuradiyyar zabe."

Kara karanta wannan

Jira Ya Kare: Kotu Ta Bayyana Ranar Da Za Ta Yi Hukunci Kan Shari'ar Nasarar Babban Gwamnan APC a Zabe

Ogun: Kotun zabe za ta yanke hukunci kan shari'ar zaben gwamnan jihar a ranar Asabar

A wani labarin, mun ji cewa k otun sauraron ƙararrakin zaɓen gwamnan jihar Ogun da ke zamanta a Abeokuta, ta sanar da ranar da za ta yanke hukunci kan ƙarar da ɗan takarar gwamna na jam'iiyyar PDP, Ladi Adebutu, ya shigar kan Gwamna Dapo Abiodun.

Jaridar Nigerian Tribune ta kawo rahoto cewa kotun ta bayyana cewa za ta yanke hukuncinta kan shari'ar a ranar Asabar, 30 ga watan Satumban 2023.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Musa avatar

Aisha Musa (Hausa writer) Aisha Musa 'yar jarida ce wacce ta kwashe shekaru biyar tana aikin gogewa a harkar yada labarai. Ta kammala karatun ta a Jami'ar Ibrahim Badamasi Babangida (IBB Lapai) a shekarar 2014 tare da digirin farko a fannin Tarihi. Aisha Editan Hausa ce wacce ke amfani da kwarewa da kwazonta don karfafawa wasu gwiwar yin aiki tukuru don cimma nasara. Ta karbi lambar yabo na gwarzuwar shekarar 2021 a bangaren Hausa na Legit. Za ku iya aika mata sakonnin imel ta adireshinta aisha.musa@corp.legit.ng