Ganduje Ya Ce Jam'iyyar APC Za Ta Lashe Zaben Gwamnan Bayelsa

Ganduje Ya Ce Jam'iyyar APC Za Ta Lashe Zaben Gwamnan Bayelsa

  • Shugaban jam'iyyar All Progressives Congress (APC) na ƙasa ya yi magana kan yiwuwar jam'iyyar ta lashe zaben gwamnan jihar Bayelsa
  • Abdullahi Umar Ganduje ya bayyana cewa jam'iyyar na da tawagar yaƙin neman zaɓe mai ƙarfi da za ta sanya ta yi nasara a zaɓen
  • Shugaban jam'iyyar.ya kuma bayyana ɗan takarar gwamnan APC na jihar, Timipre Sylva, a matsayin wanda ya san al'amuran mulki

Jihar Bayelsa - Shugaban jam'iyyar All Progressives Congress (APC) na ƙasa, Abdullahi Umar Ganduje, ya ce jam'iyyar na da gagarumar tawagar yaƙin neman zaɓe wacce za ta sanya ta lashe zaɓen gwamnan jihar Bayelsa da za a gudanar a ranar 11 ga watan Nuwamba.

Ganduje ya buƙaci ƴaƴan jam’iyyar da su yi aiki tare domin tabbatar da nasarar jam'iyyar a zaɓen, cewar rahoton Daily Trust.

Kara karanta wannan

Da Ɗumi-Ɗumi: Kotun Zaɓe Ta Ƙara Tsige Ɗan Majalisar PDP, Ta Umarci INEC Ta Canza Zaɓe

Ganduje ya magantu kan zaben gwamnan Bayelsa
Ganduje ya ce jam'iyyar APC za ta yi nasara a zaben gwamnan Bayelsa Hoto: Abdullahi Umar Ganduje
Asali: Facebook

Shugaban jam'iyyar ya bayyana haka ne a Yenagoa, babban birnin jihar Bayelsa a ranar Juma'a, 29 ga watan Satumba, yayin da yake ƙaddamar da kwamitin yaƙin neman zaɓen APC na ƙasa kan zaɓen gwamnan jihar Bayelsa, wanda gwamnan jihar Gombe, Muhammad Inuwa Yahaya ke jagoranta.

Ya ce Sylva a matsayinsa na tsohon gwamna kuma minista ya saba da aikace-aikacen gwamnati kuma zai iya ba jihar jagorancin da ake buƙata da kuma kawo cigaba.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Ya kuma buƙaci kwamitin yaƙin neman zaben da su kasance masu ɗa’a da mayar da hankali wajen cin zaɓe tare da tabbatar da cewa mulkin jihar Bayelsa ya dawo hannun APC bayan zaɓen.

APC za ta yi nasara cikin sauƙi

Shugaban kwamitin yaƙin neman zaben jam'iyyar APC na ƙasa, kuma gwamnan jihar Gombe, Mohammed Inuwa Yahaya, ya bayyana fatansa cewa jajirtattun mutanen da ke kwamitin yaƙin neman zaɓen da kuma ɗumbin goyon bayan da jam'iyyar ta samu daga al'ummar jihar Bayelsa, zaɓen zai kasance cikin sauki ga APC da ɗan takararta, Sylva.

Kara karanta wannan

Kujerar Gwamnan PDP Ta Fara Tangal-Tangal, Kotun Zaɓe Zata Yanke Hukunci Kan Zaɓen Da Ya Lashe

A nasa ɓangaren, ɗan takarar gwamna, Sylva, ya yi alƙawarin dawo da jihar kan turbar cigaba ta hanyar amfani da manufofinsa guda shida.

Kwankwaso Ya Caccaki Ganduje

A wani labarin kuma, ɗan takarar shugaban ƙasa na jam'iyyar NNPP, Rabiu Musa Kwankwaso ya caccaki Abdullahi Umar Ganduje, abokin faɗansa na siyasa.

Kwankwaso ya bayyana cewa Ganduje ba zai iya jagorantar Shugaba Tinubu ya samu nasara ba a zaɓen 2027 saboda ya zama kaya.

Asali: Legit.ng

Online view pixel