Jihar Kano: Abba Gida Gida Ya Yi Sababbin Nade-Naden Mukamai 116

Jihar Kano: Abba Gida Gida Ya Yi Sababbin Nade-Naden Mukamai 116

  • Gwamnatin Abba Kabir Yusuf ta jihar Kano ta sanar da karin nade-nade 116 a ranar Juma'a, 29 ga watan Satumba
  • Abba Gida Gida ya nada manyan hadimai na SSA, masu bada shawara na musamman da wasu wadanda za su rika taimaka masa
  • Babban sakataren yada labaran gwamnan, Sanusi Bature ya ce matasa aka fi ba wa fifiko wajen nadin mukaman

Jihar Kano - Gwamnan jihar Kano, Abba Kabir Yusuf, ya sanar da nadin karin mutum 116 a matsayin hadimansa, jaridar Daily Trust ta rahoto,

Kamar yadda jaridar Leadership ta rahoton, sabbun nade-naden da Abba Gida Gida ya yi sun hada da manyan masu ba da shawara 63, masu bayar da shawara na musamman 41 da hadimai 12.

Abba gida-gida ya nada sabbin hadimai 116
Jihar Kano: Abba Gida Gida Ya Yi Sababbin Nade-Naden Mukamai 116 Hoto: @Kyusufabba
Asali: Twitter

Hakan na kunshe ne a cikin wata sanarwa da babban sakataren yada labaran gwamnan, Sanusi Bature ya aikewa manema labarai a Kano a ranar Juma'a, 29 ga watan Satumba.

Kara karanta wannan

Duba ta cika: An kama kasurgumin dan ta'addan da ke sace mutane a jihar Arewa

Bature ya bayyana nade-naden da Gwamna Yusuf ya yi a matsayin cimma manufar sanya matasa a cikin harkar gwamnati da janyo gwamnati kusa da mutane.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Ya bayyana cewa:

"A kokarinsa na shigar da kwararru wajen samar da shugabanci na gari, Gwamna Abba Kabir Yusuf na jihar Kano ya amince da nadin manyan mataimaka na musamman, masu ba da shawara na musamman da hadimai inda aka bai wa matasa fifiko."

Ya taya sabbin wadanda aka nada mukaman murna tare da yin kira gare su da su yi aiki bisa tsarin gwamnati na sanya jama’a a gaba da komai.

NNPP Ta Rusa Kwamitin NWC Karkashin Abba Kawu Ali, Ta Amince Da Korar Kwankwaso

A wani labari na daban, kwamitin amintattu (BoT) na jam’iyyar New Nigeria Peoples Party (NNPP) ta amince da rushe kwamitin ayyuka na NWC karkashin jagorancin Abba Kawu Ali.

Kara karanta wannan

Yadda aka kamo wasu mutum 5 da suka yunkurin siyar da jariri mai kwanaki 8 a Kano

Kwamitin BoT ta kuma tabbatar da korar dan takarar shugaban kasa na jam'iyyar NNPP a zaben 2023, Sanata Rabi'u Musa Kwakwanso, rahoton Nigerian Tribune.

Hakan na kunshe ne a cikin sanarwar da aka fitar a karshen taron BoT na jam’iyyar NNPP wanda ya gudana a Otal din Rockview da ke Apapa, jihar Lagas a ranar Juma’a, 28 ga watan Satumba.

Asali: Legit.ng

Online view pixel