Budurwa Yar Najeriya Ta Yi Caraf Da Masoyinta Da Tsurut Kamar Karamin Yaro

Budurwa Yar Najeriya Ta Yi Caraf Da Masoyinta Da Tsurut Kamar Karamin Yaro

  • Wata matashiyar budurwa yar Najeriya da masoyinta dan tsurut sun dauka hankali a intanet saboda banbancin halittarsu
  • Masoyan sun yi fice a duniya bayan wasu hotunansu na soyayya ya bayyana a dandalin soshiyal midiya, wato TikTok
  • Yayin da wasu masu amfani da soshiyal midiya suka yi wa masoyan dariya wasu sun nuna sha'awarsu a gare su

Wata matashiya yar Najeriya ta haddasa cece-kuce a soshiyal midiya sakamakon bayyana hotunanta tare da sahibinta wanda ya kasance dan tsurut da shi.

Hotunan da shafin @holyson101 ya wallafa a TikTok ya nuna yadda matashiyar ta daga mutumin sama sai kace wani dan karamin yaro.

Budurwa ta daga saurayinta dan tsurut sama
Budurwa Yar Najeriya Ta Yi Caraf Da Masoyinta Da Tsurut Kamar Karamin Yaro Hoto: @holyson101
Asali: TikTok

Yayin da ta dauke shi a dukkan hotunan, wani abu da ya kasance a dukka hotunan shine murmushinsu mai ban sha'awa.

Wani rubutu da ke tattare da hotunan da daya daga cikin masoyan ta wallafa ya ce: "har abadan abada shine muradin babi."

Kara karanta wannan

Ana wata ga wata: Wike ya kori manyan jami'an hukumomi da kamfanonin FCTA

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Hotunan masoyan ya ja kudi fiye da N253k a daidai lokacin kawo wannan rahoton, inda mutane da dama suka dunga zolayar su.

Kalli bidiyon a kasa:

Martanin jama'a kan hotunan masoya

Omoyemwen ta ce:

"Kwarai har abadan abada ne muradin domin ke kadai kike da shi ba zai ci amana ba."

user1212214306550 ya ce:

"Pablo da pablet babu wanda zai raba ku za ku tsufa tare da juna."

Chuku-A-Boo-Car ya ce:

"Don Allah wani ya koya mun yadda ake dariya na tsakani da Allah."

Phi_Yin ta ce:

"Har yanzzu akwai soyayya ta gaskiya ke ce kike neman dan yahoo da kamara 3."

Himamah ta ce:

"Akwai miji ke ce kike neman wanda ya hada koma..
"Eh ke."

Afollybaeta ce:

"Muddin dai kuna kaunar junanku❤️Allah ya albarkaci auren."

Unknown ta ce:

"Abun da ya fi komai gayen ba zai samu matsalar fushi ba."

Kara karanta wannan

Yan Bindiga Sun Harbi Dalibai 3, Sun Sace Wata a Kwalejin Kimiyya a Wata Jihar Arewa

Matashi ya gwangwaje budurwarsa da sabuwar mota, iPhone 15 da fili

A wani labarin kuma, wata matashiyar budurwa ta rusa ihu sannan ta kusa shidewa bayan ta ga sabuwar motar Marsandi da saurayinta ya siya mata a matsayin kyautar zagayowar ranar haihuwarta.

An saka motar kirar Marsandi a cikin wani jan kwali. Ta kusa zaucewa a lokacin da aka mika mata makullin yayin da kawayenta suka bukaci ta saita kanta wuri daya.

Asali: Legit.ng

Online view pixel