Yanzu-Yanzu: PDP Ta Yi Nasara, Kotu Ta Yanke Hukunci Kan Zaben Gwamna a 2023

Yanzu-Yanzu: PDP Ta Yi Nasara, Kotu Ta Yanke Hukunci Kan Zaben Gwamna a 2023

  • Kotun sauraron kararrakin zaben gwamna da ke zama a jihar Delta ta tabbatar da nasarar Gwamna Sheriff Oborevwor na jam'iyyar PDP
  • Kwamitin kotun karkashin jagorancin Mai shari'a C.H. Ahuchaogu, ya kori karar da APC da dan takararta, Sanata Ovie Omo-Agege suka shigar don kalubalantar nasarar Oborevwor
  • Kotun ta ce kararsu bata da inganci domin yana kunshe ne da zarge-zarge marasa tushe balle makama

Jihar Delta - Kotun sauraron korafe-korafen zaben gwamnan jihar Delta, ta tabbatar da Gwamna Sheriff Oborevwor a matsayin halastaccen gwamnan jihar.

Jam’iyyar All Progressives Congress (APC) da dan takararta, Sanata Ovie Omo-Agege, ne suka shigar da kara gaban kotun suna kalubalantar nasarar Oborevwor na jam’iyyar Peoples Democratic Party (PDP) a zaben 2023 da ya gabata.

Kotun zaben gwamnan Delta ta tabbatar da nasarar Gwamna Sheriff
Yanzu-Yanzu: PDP Ta Yi Nasara, Kotu Ta Yanke Hukunci Kan Zaben Gwamna a 2023 Hoto: Rt Hon Sheriff Oborevwori, Senator Ovie Omo-Agege
Asali: Facebook

Da take yanke hukunci a ranar Juma'a, 29 ga watan Satumba, kotun zaben ta soke karar da Sanata Omo-Agege, ya shigar gabanta yana mai kalubalantar nasarar Gwamna Oborevwor, rahoton Vanguard.

Kara karanta wannan

Zaben Kaduna: Kotun Zabe Ta Yanke Hukunci Kan Shari'ar Zaben Gwamna, Ta Fayyace Komai Na Rudani

Gwamna Oborevwor ne ya lashe zaben gwamnan jihar Delta , inji kotun zabe

Kwamitin kotun zaben mai mutum uku karkashin jagorancin Mai shari'a C.H. Ahuchaogu, ya tabbatar da Oborevwori a matsayin wanda ya lashen zaben gwamna na ranar 18 ga watan Maris a jihar.

DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar

Kotun zaben ta riki cewa wadanda suka shigar da karar sun kasa tabbatar da zarge-zargensu na rashin bin dokar zabe da tafka magudi a zaben.

Kamar yadda Channels TV ta rahoto, kotun ta jaddada cewar karar na kunshe da zarge-zargen da ba su da tushe balle makama, inda ta yi nuni da cewa ba ta da inganci.

Ashiru Kudan zai daukaka kara zuwa kotun gaba don neman hakkin 'yan jihar Kaduna

A wani labarin kuma, mun ji cewa dan takarar gwamna a jam'iyyar PDP a jihar Kaduna, Isa Ashiru Kudan ya ce zai daukaka kara kan shari'ar da aka yi.

Kara karanta wannan

Kujerar Gwamnan PDP Ta Fara Tangal-Tangal, Kotun Zaɓe Zata Yanke Hukunci Kan Zaɓen Da Ya Lashe

A jiya ne kotun sauraran kararrakin zaben jihar ta yanke hukunci inda ta tabbatar da nasarar Gwamna Uba Sani na jam'iyyar APC, Daily Trust ta tattaro.

Ashiru Kudan na kalubalantar zaben Gwamna Uba Sani da aka gudanar a watan Maris na farkon wannan shekara.

Asali: Legit.ng

Online view pixel