Manyan Labarai A Yau
Tsohon mataimakin kakakin jam'iyyar APC na ƙasa, Timi Frank ya yi aike da saƙo mai muhimmanci ga alƙalan kotun ƙoli da za su saurari shari'ar Atiku da Tinubu.
Rundunar ƴan sandan jihar Borno ta fara gudanar da bincike bayan kwamishinan jihar ya yi mutuwar bazata a cikin gidansa da ke birnin Maiduguri, babban birnin jihar.
Sanata Shehu Sani, tsohon sanatan da ya wakilci Kaduna ta tsakiya, ya nemi sanin wacce kotu ministar mata za ta kai majalisar ɗinkin duniya ƙara.
An samu aukuwar wani hatsarin jirgin ruwa a ƙaramar hukumar Katcha ta jihar Neja. Hatsarin ya yi sanadiyyar rasuwar yaro ɗaya yayin da wasu da dama suka ɓace.
Ministan babban birnin tarayya, Nyesom Wike ya amince da kwace gidajen da hukumar babban birnin tarayya ta siyarwa mutane amma suka sauya akalar amfaninsu.
Rundunar ƴan sandan jihar Borno ta sanar da cafke wasu mutum biyu da ake zargi da laifin hannu a halaka ɗiyar wani ɗan majalisar dokokin jihar Borno.
Dakarun sojojin Najeriya sun samu nasarar yin galaba akan ƴan ta'adda a sassan daban-daban na ƙasar nan. Sojojin sun kuma cafke masu taimakawa ƴan ta'addan.
Gwamnan jihar Ƙatsina, Alhaji Dikko Umaru Radda, ya sha alwashin ɗaukar mataki mai tsauri kan duk wanda aka samu yana taimakon ƴan bindiga a jihar.
Wata budurwa ƴar Najeriya ta bayyana cewa ta auri mijin da take so wanda ya kwanta mata a zuciya, inda ta ƙi yarda da batun masu cewa tsoho ta aura.
Manyan Labarai A Yau
Samu kari