Shehu Sani Ya Yi Martani Bayan Ministar Tinubu Ta Yi Barazanar Kai UN Kara

Shehu Sani Ya Yi Martani Bayan Ministar Tinubu Ta Yi Barazanar Kai UN Kara

  • Tsohon sanata, Sanata Shehu Sani ya tambayi Uju Kennedy-Ohanenye, kotunan da take shirin kai ƙarar majalisar ɗinkin duniya.
  • Sani ya bayyana hakan ne biyo bayan barazanar da ministar harkokin mata ta yi na gurfanar da majalisar ɗinkin duniya a gaban kotu kan zargin almundahana da kuɗade
  • Kennedy-Ohanenye ta umarci ƙungiyoyin bayar da agaji na majalisar ɗinkin duniya da su bayar da bayanan asusun da suka yi amfani da su wajen samo kuɗaɗe

FCT, Abuja - Tsohon Sanatan Kaduna ta tsakiya, Sanata Shehu Sani, ya mayar da martani kan barazanar da ministar harkokin mata, Uju Kennedy-Ohanenye ta yi na gurfanar da majalisar ɗinkin duniya (UN) a gaban kotu.

Kennedy-Ohanenye ta yi barazanar kai ƙarar majalisar ɗinkin duniya kan zargin almundahana da kudade.

Shehu Sani ya yi martani ga ministar Tinubu
Shehu Sani ya yi martani ga ministar mata, Uju Kennedy Hoto: @ShehuSani/@BarrUjuKennedy
Asali: Twitter

Da take jawabi yayin wani taron manema labarai a ranar Litinin, 16 ga watan Oktoba a Abuja, ministan ta ce ya kamata dukkan ƙungiyoyin majalisar ɗinkin duniya su baiwa gwamnati duk asusun da suka yi amfani da su wajen samo kuɗaɗe.

Kara karanta wannan

Rundunar Yan Sanda Ta Cafke Wadanda Ake Zargi da Kisan Diyar Dan Majalisa

Da yake mayar da martani kan barazanar da ministar shugaban ƙasa, Bola Tinubu ta yi na kai ƙarar majalisar dinkin duniya, Sani ya tambayi kotunan da ta shirya amfani da su wajen shigar da ƙarar ta.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Tsohon dan majalisar ya yi wannan tambayar ne ta shafinsa na X (wanda aka fi sani da Twitter) @ShehuSani, a ranar Juma'a, 20 ga watan Oktoba.

A kalamansa:

"Ministar da ta yi barazanar kai ƙarar majalisar ɗinkin duniya, ban san wanne daga cikin kotunan da take son amfani da su ba."

Ƴan Najeriya sun yi martani

Wasu ƴan Najeriya sun mayar da martani kan barazanar da ministar Tinubu ta yi a karkashin tubutun da Sani ya yi.

@SunnetplanetC ya rubuta:

"Ta cika surutu... UN ta ba NGO ɗin ku kuɗaɗe domin rabawa mutane.... NGO ɗin ku mai rijista sun cinye kuɗin ... Ba ku nemi jin ba'asi daga wajensu ba, kun ce UN ta zo ta yi bayani."

Kara karanta wannan

Bazoum: Shugaban Nijar da Aka Hamɓarar Ya Yi Yunkurin Tserewa Daga Hannun Sojoji, Bayanai Sun Fito

@kenstine ya rubuta

"Ba ta ma san abin da majalisar ɗinkin duniya ke nufi ba. Tana so ta kai karar duniya, ciki har da kanta."

@BillyAjala ya rubuta:

"Za a iya kai ƙarar majalisar ɗinkin duniya kotu inda aka aikata laifi, za a iya ɗaukar mataki a kansu a Najeriya kamar yadda aka ɗauki mataki kan galibin kamfanonin ƙasashen waje kamar su Mobil, Shell, Chevron da kuma biyan diyya ga waɗanda abin ya shafa a Najeriya."

Shehu Sani Ya Yi Martani Ga Gumi

A wani labarin kuma, tsohon sanatan Kaduna ta tsakiya, Sanata Shehu Sani, ya yi martani ga Sheikh Ahmad Abubakar Gumi, bayan ya kira Wike da shaiɗanin mutum.

Shehu ya bayyana cewa bai kamata aƴi amfani da addini ba wajen.caccakar ministan na birnin tarayya Abuja.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng