Shugaba Tinubu Ya Ce Da Ba a Cire Tallafin Man Fetur Ba, da Jiihohi Sun Kasa Samun Kudade

Shugaba Tinubu Ya Ce Da Ba a Cire Tallafin Man Fetur Ba, da Jiihohi Sun Kasa Samun Kudade

  • Shugaban ƙasa Bola Ahmed Tinubu ya kare matakin da gwamnatinsa ta ɗauka na tsige tallafin man fetur
  • Shugaban ƙasar ya bayyana cewa da cire tallafin ya zamo tilas ne domin ceto ƙasar nan daga durƙushewa
  • A cewar shugaban ƙasar wahalhalun da ake sha a yanzu na.wucin gadi ne, kuma sauƙi na nan tafe nan gaba

FCT, Abuja - Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya ce manufofi da tsare-tsare na gwamnatinsa na da burin ganin an samu al'umma mai adalci, inganci da gaskiya, cewar rahoton Daily Trust.

Da yake jawabi a lokacin da yake ganawa da tawagar wakilai na Musulmin Kudu maso Yamma ƙarkashin jagorancin Alhaji Rasaki Oladejo a fadar shugaban ƙasa da ke Abuja, Tinubu ya ce akwai bukatar sadaukarwa ga ƙasa domin samun cigaba.

Kara karanta wannan

Sheikh Ahmad Gumi Ya Ɗebo da Zafi, Ɗan Majalisar Tarayya Ya Maida Masa da Zazzafan Martani

Shugaba Tinubu ya yi magana kan cire tallafin man fetur
Shugaba Tinubu ya yi magana kan cire tallafin man fetur da gwamnatinsa ta yi Hoto: @DOlusegun
Asali: Twitter

Meyasa gwamnatin Tinubu ta cire tallafin man fetur?

A kalamansa:

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

"Magana ce ta makomarmu. Dole ne mu tabbatar mun kare makomarmu. Allah ba zai ɗora mana wani nauyi da ba za mu iya ɗauka ba. Ya sanya mu a nan domin wata manufa."
"Yana iya zama da wahala amma abubuwa za su gyaru. Mun kauce masa (cire tallafin man fetur) tsawon shekaru 40. Yanzu duk muna cikin wahala, amma domin kada Najeriya ta durkushe, sai da muka cire tallafin."
“A tarihin ƙasashen da suka yi nasara, babu wani abu da ya fi dacewa da shugabancin al'umma wajen ɗaukar matakai masu tsauri a daidai lokacin da ya kamata da kuma dalilan da suka dace. Da jihohi sun koma ba su samun kuɗaɗe

Shugaban, wanda ya ce ƙalubalen da al’ummar kasar ke fuskanta a halin yanzu na wucin gadi ne, ya kuma tabbatar wa ƴan Nijeriya cewa, kwanaki masu kyau suna nan zuwa a gaba.

Kara karanta wannan

Gwamnatin Shugaba Tinubu Ta Fara Kukan Babu Kuɗi a Ƙasa, Ta Ce da Kame-Kame Ake Biyan Albashi

"Dole ne mu yi imani da ƙasa ɗaya, dole ne mu yi imani da Najeriya. Za mu yi iya ƙoƙarinmu, kuma tattalin arzikinmu zai inganta domin amfanin ƴan Najeriya. Ina da tabbacin hakan, kuma muna kan aiki domin tabbatar da hakan." A cewarsa.

Gwamnatin Tinubu Ta Ca Babu Kudi a Kasa

A wani labarin kuma, gwamnatin tarayya ta bayyana cewa ta faɗa cikin wani yanayi na samun ƙarancin kuɗaɗe.

Gwamnatin ta bayyana cewa biyan albashin ma'aikata yanzu ya koma jan aiki a wajenta, domin da ƙyar take iya biyansu haƙƙinsu.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng

Online view pixel