Yan Sanda Sun Kama Shugaba Da Mataimakin Shugaban Makaranta Kan Dukan Dalibi Har Lahira a Zaria
- Jami'an yan sandan jihar Kaduna sun kama shugaba da mataimakin shugaban makarantar Al-Azhar da ke Zaria
- An kama wadanda ake zargin ne bayan mutuwar wani dalibin JSS3, Marwanu Nuhu Sambo a ranar Juma'a, 20 ga watan Oktoba
- An tattaro cewa shugaban makarantar, mataimakinsa da wani dalibin babban aji ne suka yi wa marigayin duka har lahira saboda fashin zuwa aji
Zaria, jihar Kaduna - An kama shugaba da mataimakin shugaban makarantar Al-Azhar da ke Zaria, jihar Kaduna kan zargin dukan dalibin JSS3, Marwanu Nuhu Sambo har lahira.
An yi zargin cewa wadanda ake zargin sun hadu sun yi wa Sambo hukunci mai tsanani wanda ya yi sanadiyar mutuwarsa a ranar Juma'a, 20 ga watan Oktoba, rahoton The Nation.
An yi zargin cewa shugaba, mataimakin shugaba da wani shugaban dalibai na makarantar Al-Azhar ne suka yi wa Sambo dukan tsiya kan fashin zuwa aji.
Kakakin yan sandan jihar Kaduna, ASP Mansir Hassan, ya tabbatar da kamun mutanen.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Ya ce:
"An kama mutum biyu da ake zargi a lamarin. Kwamishinan yan sandan ya yi umurnin gudanar da cikakken bincike kan lamarin kuma za mu kamo bakin zaren."
An yi zargin cewa an yi wa marigayin horo mai tsanani ciki harda bulala sama da guda 100.
Wata majiya ta ce:
"Daga bisani shugaban makarantar ya mika shi ga wasu shugabannin dalibai wadanda suka ci gaba da dukansa da sanduna har sai daya daga cikin hakoranta ya fita. A wannan gabar ne marigayin ya koma babu yadda yake.
"Amma maimakon kai shi asibiti cikin gaggawa, sai shugabannin daliban suka yasar da shi a harabar makarantar kusa da bandakin maza har zuwa lokacin tashi daga makaranta...
"Kukan sauran daliban makarantar da suka ga abun da ya wakana ne ya ja hankalin sauran malamai wadanda suka gaggauta zuwa wajen inda suka tarar da gawan yaron."
Wata majiya ta ce daliban sun gaggauta kai shi wani asibiti mai zaman kansa a Zaria inda aka tabbatar da mutuwarsa.
Kotu ta daure malami a kurkuku saboda ya zane daliba mace da bulala
A wani labarin, Legit Hausa ta rahoto a baya cewa hukumar 'yan sandan Najeriya ta gurfanar da wani malamin makaranta ɗan kimanin shekara 43, David Yusuf, a gaban Kotun Majistire mai zama Wuse II a Abuja ranar Taata.
Jaridar Vanguard ta wallafa a shafinta na Manhajar X cewa an gurfanar da Malamin ne bisa tuhumar ya zane ɗaliba mace a makarantar Sakandiren mata da ke Kuje.
Asali: Legit.ng