An Sako Yar Bautar Kasar da Aka Sace a Jihar Zamfara

An Sako Yar Bautar Kasar da Aka Sace a Jihar Zamfara

  • Hukumar kula da masu yi wa ƙasa hidima (NYSC) ta sanar da ceto ɗaya ɗaga cikin ƴan matan masu yi wa ƙasa hidima da aka sace a Zamfara
  • Hukumar ta ce ta samu nasarar ceto ƴar bautar ƙasar ne a ranar Juma'a, 21 ga watan Oktoban bayan ta shafe kwanaki a tsare
  • Har yanzu dai akwai sauran masu yi wa ƙasa hidima da aka sace a jihar Zamfara tare da direbansu a kan hanyarsu ta zuwa Sokoto

FCT, Abuja - Hukumar kula da matasa masu yi wa kasa hidima ta ƙasa (NYSC) ta ce ta samu nasarar ceto ɗaya daga cikin ƴan mata bakwai da aka yi garkuwa da su a Zamfara.

Kakakin hukumar ta NYSC, Eddy Megwa, ne ya bayyana hakan a wata sanarwa da ya fitar ranar Asabar, 21 ga watan Oktoba, cewar rahoton The Punch.

Kara karanta wannan

Dakarun Sojoji Sun Samu Galaba Kan Yan Ta'adda, Sun Tura Masu Yawa zuwa Barzahu

An sako yar bautar kasar da aka sace
An saki yar bautar kasar da aka sace a Zamfara Hoto: NYSC
Asali: Twitter

A cewar sanarwar, an ceto ƴar bautar ƙasar ne a daren Juma'a, 20 ga watan Oktoba da misalin ƙarfe 12:30 na dare “ta hanyar taimakon jami'an tsaro”, yayin da ya bayyana kwarin gwiwar cewa za a sako sauran ƴan matan da aka sace.

Yadda aka ceto mai yi wa ƙasa hidimar

Wani bangare na sanarwar na cewa:

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

"Hukumar hukumar kula da masu yi wa ƙasa hidima ta ƙasa na son sanar da jama'a cewa, hukumar ta hanyar taimakon jami'an tsaro a ranar Juma'a, 20 ga watan Oktoba, 2023 da misalin karfe 12:30 na rana ta ceto ɗaya daga cikin ƴan matan da aka yi garkuwa da su a Zamfara, daga cikin bakwai da aka sa ce har da direban motar."
"Hukumar na da yaƙinin cewa tare da haɗin gwiwar hukumomin tsaro, za a sako sauran."

Kara karanta wannan

Gwamnan Jihar Arewa Ya Fara Binciken Sarakunan Gargajiya Masu Taimakawa Yan Bindiga a Jiharsa

A baya an sako wasu daga cikin ƴan matan

A ranar 19 ga watan Agustan 2023 ne wasu ƴan bindiga suka yi garkuwa da wasu masu yi wa ƙasa hidima guda takwas a kan babban titin hanyar jihar Zamfara, a hanyarsu ta zuwa sansanin NYSC da ke Sokoto.

Tun da farko dai hukumar NYSC ta sanar da sakin uku daga cikin ƴan NYSC ɗin da aka sace a ranar 18 ga watan Satumban 2023, wata ɗaya bayan sace su.

Yanzu haka dai sauran masu yi wa ƙasa hidimar sun shafe kwanaki 60 a hannun ƴan bindiga tun bayan sace su a watan Agusta.

Za a Biya Yan NYSC N245k a Taraba

A wani labarin kuma, gwamnatin jihar Taraba ta sanar da cewa za ta fara biyan masu yi wa ƙasa hidima a jihar kuɗaɗe har N245.

Zainab ta ce daga cikin alawus din dubu 50 na kula da lafiya ce sai kuma dubu 25 na wurin zama da kuma dubu 10 tallafawa daga jiha.

Asali: Legit.ng

Online view pixel