Manyan Labarai A Yau
Shugaban Jamhuriyar Nijar da sojoji suka kifar da gwamnatinsa, Mohammed Bazoum, ya yi yunkurin gudowa daga tsare zuwa Najeriya inji gwamnatin soji.
Ministan babban birnin tarayya, Nyesom Wike, ya magantu game da soyayyar da yake yi wa girki. Tsohon gwamnan na jihar Ribas ya ce yana alfahari da iya girki.
Mutane da dama ciki harda jami’in dan sanda sun jikkata yayin da magoya bayan jam’iyyar APC da SDP suka yi musayar wuta a karamar hukumar Idah ta jihar Kogi.
Wata mummunar gobara da ta tashi a rukunin wasu shaguna a wata kasuwar birkin Calabar na jihar Cross Rivers ta janyo asarar dukiya mai tarin yawa.
Gwamnan jihar Borno, Babagana Umara Zulum ya ba da wa’adin awa 72 a rushe gidajen karuwai da matattarar bata-gari a Maiduguri, babban birnin jihar.
Yayin da ake takaddama kan zaben gwamna a jihar Kano, wani shahararren malamin addini, Primate Elijah Ayodele, ya yi hasashen cewa APC ce za ta yi nasara a kotu.
Sheikh Ahmad Gumi ya bayyana ministan babban birnin tarayya, Nyesom Wike, a matsayin shaidanin mutum kan tarban ambasadan Isra’ila a Najeriya a ofishinsa.
Tsohon Sanatan Kaduna ta tsakiya, Shehu Sani, ya ce maganar da Sheikh Ahmad Gumi ya yi na kiran Nyesom Wike da shaidani abu ne da ba za a amince da shi ba.
Wasu miyaguun ƴan bindiga sun salwantar da rayukan mutum biyar a wani ƙazamin harin ta'addanci da suka kai a jihar Benue. Hukumomi sun tabbatar da hakan.
Manyan Labarai A Yau
Samu kari