Budurwa Yar Najeriya Ta Yi Wuff Da Wani Dattijon Bature, Hotunansu Sun Yadu

Budurwa Yar Najeriya Ta Yi Wuff Da Wani Dattijon Bature, Hotunansu Sun Yadu

  • Wata budurwa ƴar Najeriya ta yi martani ga masu cewa ta auri wani tsoho saboda shi bature ne
  • Hakan na zuwa ne bayan ta saka wani hoton bidiyo da ke nuna mijinta jim kaɗan bayan aurensu na gargajiya
  • Wani ya yi nuni da cewa budurwar ta zaɓi ta auri bature duk da ya girme ta, amma ba ta yarda ba

Wata budurwa ƴar Najeriya da ta auri wani bature ta garzaya manhajar TikTok domin ta nuna shi ga mabiyanta.

Sai dai, wasu masu amfani da TikTok sun nuna cewa mutumin ya girmi budurwa nesa ba kusa ba, wanda hakan bai yi mata daɗi ba.

Budurwa yar Najeriya ta auri bature
Budurwar ta caccaki masu cewa ta auri tsoho Hoto: TikTok/@nkirukaofuma
Asali: TikTok

A wani martani da ta yi cikin wani sabon bidiyo, budurwar mai suna Nkeiruka ta gaya wa mutanen da ke sukanta cewa su je su nemo na su mazajen auren.

Kara karanta wannan

Gobara Ta Lakume Rayukan Mutane 2 a Gidan Mai Yayin Da Ake Tsaka da Tsadar Man Fetur, An Bayyana Dalili

Nkeiruka ta ce ta samu nasarar samun mijin nata ta kuma yi wa masu caccakarta martanin cewa su ma su je su nemo na su wanda suke ganin ya cancanta.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Bidiyoyin da ta sanya a TikTok sun nuna cewa budurwar da baturen mijin nata sun yi auren gargajiya ne.

Wane irin martani ƴan soshiyal midiya suka yi?

Masu amfani da TikTok sun mayar da martani ga bidiyon budurwar da ta auri wani bature

@GIFTY ya rubuta:

"Wannan mutumin ba tsoho bane. Kuna so ta auri ƙaramin yaro ɗan Yahoo ko menene ku ke nufi? Omoh maganar aure ake ba maganar soyayya ba."

@Maryam ta rubuta:

"Don Allah idan abokan mijinki basu da aure ina ciki."

@Nemereafrik ta yi tambaya:

"Don Allah yana da babban yaya?"

@Sonita Geh ta rubuta:

"Mutanen da ba su da kan gado koda yaushe cike suke da shirme."

Kara karanta wannan

Innalillahi: Mutane Sama da 35 Sun Mutu Yayin da Wasu Akalla 40 Suka Jikkata a Hatsari a Arewa

@kadirose ya mayar da martani:

"Kiji daɗin mijinki, karki damu da maganganun mutane."

@Melunga ya rubuta:

"Ƴan baƙin ciki, jin zafi kawai suke yi, ki ji daɗin ki ƴar uwa."

Mata Ta Samu Juna Biyu Daga Tausa

A wani labarin kuma, wata budurwa ƴar Najeriya ta bayyana yadda ta samu jun biyu daga cewa mijinta ya yi mata tausa.

Budurwar mai suna Adebola a cikin wani bidiyo, ta ce ta nemi mijin ya matsa mata jiki ne kawai, kafin ta ankara sai gata da juna biyu.

Asali: Legit.ng

Online view pixel