Mutum 7 Sun Rasu a Wani Mummunan Hatsarin Mota a Jihar Osun

Mutum 7 Sun Rasu a Wani Mummunan Hatsarin Mota a Jihar Osun

  • Wani mummunan hatsarin mota da ya auku a jihar Osun ya yi sanadiyyar rasuwar wasu matafiya mutum bakwai
  • Hatsarin motar wanda aka yi a kan titin Osogbo/Gbongan ya auku ne a sakamakon ƙwacewar da motar ta yi wa direban saboda tsananin gudu
  • Kwamandan hukumar kiyaye haɗura a jihar Osun wanda ya tabbatar da aukuwar harin, ya shawarci direbobi da su riƙa tuƙi cikin tsanaki

Jihar Osun - Wasu matafiya mutum bakwai sun rasa rayukansu yayin da wasu mutum uku suka samu raunuka a wani hatsarin mota da ya auku a hanyar ƙauyen Ogidi, da ke kan titin Osogbo/Gbongan a jihar Osun.

Hatsarin ya shafi wata mota ƙirar Nissan Sharon mai kalar toka, mai lamba WWD57AE, kamar yadda jaridar Channels tv ta rahoto.

Rayuka sun salwanta a hatsarin mota a Osun
Rayukan mutum 7 suka salwanta a hatsarin Hoto: FRSC
Asali: UGC

Wani ganau ba jiyau ba ya ce direban motar wanda yake kan hanyarsa ta zuwa Odeomo daga Osogbo, yana cikin tsananin gudu sai motar ta ƙwace masa ya faɗa cikin rami.

Kara karanta wannan

Gwamnan Arewa Ya Waiwayi Leburori, Ya Ce Zai Ɗauki Nauyin Karatunsu Har Su Gama Jami'a Bisa Sharaɗi 1

Hukumomi sun tabbatar da aukuwar lamarin

Kwamandan hukumar kiyaye haɗura (FRSC) a jihar Osun, Henry Benamaisai ya tabbatar da aukuwar lamarin a ranar Asabar, 21 ga watan Oktoban 2023.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

An garzaya da waɗanda suka jikkata zuwa asibitin koyarwa na jami'ar jihar Osun a Osogbo, yayin da aka ajiye gawarwakin waɗanda suka mutu a ɗakin ajiye gawa na asibitin." A cewarsa.

Ya ce jami’an rundunar ƴan sandan Najeriya sun taimakawa jami’an FRSC wajen gudanar da aikin.

Ya ƙara da cewa an gano jakunkuna biyu dauke da kaya daga wurin da hatsarin ya auku.

Kwamandan na FRSC, ya shawarci masu ababen hawa da su riƙa tuka mota a hankali tare da bin duk ƙa’idojin hanya domin gujewa aukuwar haɗura a hanyoyin wanda ke haifar da asarar rayuka da dukiyoyi.

Gwamna Ya Rasa Hadimi a Hatsarin Mota

Kara karanta wannan

'Yan Bindiga Sun Yi Kwantan Ɓauna, Sun Kai Hari Kan Ayarin Ɗan Takarar Gwamna a Jihar Arewa

A wani labarin na daban kuma, gwamnan jihar Katsina, Malam Dikko Umaru Radda, ya rasa hadiminsa a wani hatsarin mota da ya auku a hanyar Kaduna zuwa Katsina.

Dakta Shamsuddeen Abubakar mai taimakawa gwamnan kan harkokin addinin musulunci, ya rasu ne lokacin da yake kan hanyarsa ta zuwa birnin Katsina daga Kaduna.

Asali: Legit.ng

Online view pixel