Borno: Yan Sanda Sun Fara Bincike Kan Mutuwar Kwamishina

Borno: Yan Sanda Sun Fara Bincike Kan Mutuwar Kwamishina

  • Rundunar ƴan sandan jihar Borno ta fara gudanar da bincike bayan sabon kwamishinan da aka naɗa a jihar ya rasu
  • Engr. Ibrahim Idris Garba wanda ke riƙe da muƙamin kwamishinan gyara, sake ginawa da sake matsuguni na jihar ya yi rasuwar bazata a ranar Asabar
  • Gwamna Babagana Umara Zulum na jihar ya aike da saƙon ta'aziyyarsa ga iyalai da abokan arziƙin marigayin kwamishinan

Jihar Borno - Kwamishinan gyara, sake ginawa da sake matsuguni (RRR) na jihar Borno, Engr. Ibrahim Idris Garba, ya riga mu gidan gaskiya.

Kwamishinan ya rasu ne a safiyar ranar Asabar, 21 ga watan Oktoba, a gidansa da ke rukunin gidajen 777 da ke cikin birnin Maiduguri, babban birnin jihar.

Yan sanda sun fara bincike kan mutuwar kwamishina a Borno
Yan sanda sun fara bincike kan rasuwar kwamishina a Borno Hoto: @ZagazOlaMakama/Nigerian Police Force
Asali: UGC

A halin yanzu, rundunar ƴan sandan jihar Borno ta fara “binciken gaggawa” kan mutuwar kwamishinan, cewar rahoton jaridar Leadership.

Kara karanta wannan

Sabon Kwamishina Da Aka Nada a Kwanakin Nan Ya Riga Mu Gidan Gaskiya, An Bayyana Dalilin Mutuwarsa

Gwamna Zulum ya yi ta'aziyya

Jaridar The Punch ta tattaro cewa mai magana da yawun gwamna Babagana Umara Zulum, Malam Isa Gusau ne ya bayyana hakan a wata sanarwa da ya raba wa manema labarai ranar Asabar, 21 ga watan Oktoban 2023.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Gusau ya yi nuni da cewa kwamishinan ƴan sandan jihar ya ziyarci gidan da Engr. Garba ya rasu ne a Maiduguri a ranar Asabar.

Sanarwar da Gusau ya fitar na cewa:

"Gwamna Babagana Umara Zulum ya samu labarin cikin kaɗuwa da baƙin ciki matuƙa. Gwamnan ya jajanta tare da iyalan marigayi kwamishinan, sauran masoya, abokan arziƙi, abokan hulɗa, da mambobin majalisar zartarwa ta jihar."
"Marigayi Engr Ibrahim Idris Garba  ya kasance mai baiwa gwamna shawara na musamman kan ayyuka na musamman kafin daga bisani a naɗa shi kwamishinan RRR, a lokacin da Zulum ya fara wa'adi na biyu na mulkinsa."

Kara karanta wannan

Rundunar Yan Sanda Ta Cafke Wadanda Ake Zargi da Kisan Diyar Dan Majalisa

"Allah ya gafarta wa kwamishinan kurakuran sa, ya shigar da shi Aljanna."

Yan Sanda Sun Cafke Wadanda Ake Zargi da Kisan Diyar Dan Majalisa

A wani labarin kuma, rundunar ƴan sandan jihar Borno ta cafke mutum biyu da ake zargi da hannunsu a kisan ɗiyar dan majalisar dokokin jihar Borno.

Rundunar ƴan sandan ta cafke mijin matar tare da abokinsa waɗanda su ne suka kai gawarta zuwa ofishin ƴan sanda.

Asali: Legit.ng

Online view pixel