Manyan Labarai A Yau
Jami’an hukumar NSCDC a babban birnin tarayya Abuja sun harbi dalibai biyu. Abun ya afku ne da misalin karfe 11:20 na safe a ranar Laraba, 29 ga watan Nuwamba.
Jami’an hukumar kwastam na Najeriya a jihar Ogun, sun kama alburusai 975 da aka nade a cikin buhunan shinkafa a ranar Litinin, 27 ga watan Nuwamba.
An samu asarar rayukan bayin Allah bayan aukuwar wani mummunan hatsarin mota a jihar Kwara. Mutum 25 sun riga mu gidan gaskiya yayin da wasu suka raunata.
Majalisar dokokin jihar Bauchi ta zabi sabon kakakin majalisa da mataimakinsa bayan kotin daukaka kara ta soke zaben tsohon kakakin majalisar da mataimakinsa.
Shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu ya isa majalisar tarayya domin gabatar da kasafin kudi na shekarar 2024 a ranar Laraba, 29 ga watan Nuwamban 2023.
Kotun daukaka kara ta tabbatar da nasarar yar majalisar jam'iyyar APC, Rukayat Motunrayo Shittu, mai wakiltar mazabar Owode/Oniru a majalisar dokokin jihar Kwara.
Wata mai siyar da kayan gwanjo ta cika da mamaki bayan da ta tsinci N1.5m a cikin kayan gwanjon da ta siyo. Yan Najeriya sun yi martani sosai a kan hakan.
An samu asarar rayuka a wani mummunan hatsarin mota da ya auku a jihar Kebbi. Hatsarin wanda ya ritsa da motar tirela ya salwantar da rayukan mutum 11.
Jam'iyyar Labour Party (LP) ta zargi kotun koli da kasa yanke hukunci a karar da Peter Obi ya daukaka. Jam'iyyar ta bayyana hakan a matsayin abun takaici.
Manyan Labarai A Yau
Samu kari