Yan Bindiga Sun Halaka Mafarauta 18 a Wani Kazamin Artabu

Yan Bindiga Sun Halaka Mafarauta 18 a Wani Kazamin Artabu

  • Rayukan mafarauta 18 sun salwanta a yayin wani artabu da miyagun ƴan bindiga da ke ɗauke da miyagun makamai a jihar Taraba
  • Ƴan bindigan sun halaka mafarautan ne a lokacin da suka yi yunƙurin kai farmaki a ƙaramar hukumar Bali
  • Shugaban mafarautan jihar wanda ya tabbatar da kisan mafarautan ya buƙaci gwamnati da ta ba su makamai masu kyau

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi

Jihar Taraba - Ƴan bindiga sun kashe mafarauta 18 a wani harin da suka kai a ƙaramar hukumar Bali da ke jihar Taraba.

Jaridar Daily Trust ta rahoto cewa an kashe mafarautan 15 ne a wata arangama da ƴan bindiga a wani dutse kusa da garin Maihula a ranar Talata, 28 ga watan Nuwamba.

Kara karanta wannan

Jami'an tsaro sun sheke dan bindiga da ceto mutum 3 da aka sace

Yan bindiga sun halaka mafarauta a Taraba
Yan bindiga sun kashe mafarauta 18 a Taraba Hoto: @PoliceNG
Asali: Twitter

An tattaro cewa ƴan bindigan da yawansu ya haura 200 sun yi yunƙurin kai hari a garin Bali hedikwatar ƙaramar hukumar Bali da wasu ƙauyukan da ke kewaye amma mafarautan sun yi artabu da su.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Ƴan bindigan waɗanda suke ɗauke da miyagun bindigu da suka fi na mafarautan, sun halaka mafarauta 15 a yayin artabun.

Wani majiya a yankin mai suna Musa Umar ya bayyana cewa mafarauta 14 ne suka mutu a wurin artabun, yayin da wasu mafarauta da dama suka samu raunuka, ɗaya kuma ya mutu a hanyar zuwa Asibitin Jalingo wanda adadin ya kai 15.

Me nene abin da hukumomi suka ce kan harin?

Shugaban kungiyar mafarauta na jihar Taraba, Adamu Dantala ya bayyana cewa an kashe mambobinsa 15 a wata arangama da ƴan bindiga.

Ya ce ƴan bindigan sun kuma yi wa mambobinsa kwanton ɓauna a kusa da garin Dakka a ƙaramar hukumar Bali inda suka kashe mafarauta uku.

Kara karanta wannan

Yan bindiga sama da 300 sun kewaye babban birnin jihar arewa, sun kashe jami'an tsaro sama da 20

"Muna buƙatar goyon bayan gwamnati da al’umma na ba mafarauta makamai domin ba a ba mu wani ƙudi domin tallafa wa iyalan waɗanda aka kashe ko kuma jinyar waɗanda suka jikkata." A cewarsa.

Basaraken masarautar Kur Bali, Alhaji Mahamud Abubakar, inda aka kashe mafarauta 15 ya bayyana cewa ƴan bindigan sun mamaye masarautarsa ​​ne tare da yunƙurin mamaye garin Bali amma mafarauta suka tare su inda suka kashe mafarauta 15.

Kakakin rundunar ƴan sandan jihar, SP Usman Abdullah bai amsa kiran wayarsa ba ko dawo da amsar saƙon da aka tura masa ta waya ba.

Legit Hausa ta samu jin ta bakin wani mazaunin birnin Jalingo, mai suna Malam Hassan wanda ya koka kan yadda hare-haren ƴan bindiga ke ƙara yawaita a jihar.

Malam Hassan ya yi bayanin cewa lamarin rashin tsaro yana ta ƙara taɓarɓarewa a jihar inda yanzu ya koma har tare hanya ake yi a kwashe mutane tare da kai musu farmaki a ƙauyukansu.

Kara karanta wannan

Yan bindiga sun halaka mutum 7 a wani kazamin hari da suka kai a wasu kauyuka 2

Ya yi kira ga gwamnati da ta ƙara zage damtse domin kawo ƙarshen matsalar rashin tsaron wacce ke kawo koma baya ga tattalin arziƙin jihar.

Ƴan Bindiga Sun Halaka Manoma

A wani labarin kuma, kun ji cewa wasu miyagun ƴan bindiga sun kai farmaki a yankin Yangtu na jihar Taraba inda suka halaka manoma biyu.

Ƴan bindigan sun ritsa manoman ne lokacin da suke tsaka da aiki a gonakinsu, wanda hakan ya sanya fargaba a zukatan mutanen yankin.

Asali: Legit.ng

Online view pixel