Jami’an Kwastam Sun Gano Muggan Makamai a Cikin Buhunan Shinkafa, Hotuna Sun Bayyana

Jami’an Kwastam Sun Gano Muggan Makamai a Cikin Buhunan Shinkafa, Hotuna Sun Bayyana

  • Jami'an hukumar kwastam sun yi babban kamu cike da nasara a karamar hukumar Imeko Afon ta jihar Ogun
  • An kama wasu harsasai da aka nade a cikin buhunan shinkafa guda biyar a wani jeji da ke titin Palace/Ayetoro
  • Nasarar ya biyo bayan bayanan sirri da hukumar ta samu bayan shafe kimanin mako guda tana bibiyar masu fasa kaurin makaman

Jihar Ogun - Jami'an hukumar kwastam reshen Ogun, sun kama harsasai da aka nade a cikin buhunan shinkafa biyar sannan aka boye su a wani jeji a hanyar Palace/Ayetoro da ke karamar hukumar Imeko Afon ta jihar.

An cafke kayan ne a ranar Litinin, 27 ga watan Nuwamba, bayan samun wasu bayanan sirri wanda ya kai ga tura wasu jami'ai yankin domin tinkarar wadanda ke shigo da makaman cikin kasar.

Kara karanta wannan

Yan fansho ga Tinubu: Cire tallafin mai ya jefa mu cikin mawuyacin hali

Jami'an kwastam sun kama muggan makamai a buhunan shinkafa
Jami’an Kwastam sun gano muggan makamai a cikin buhunan shinkafa Hoto: @CustomsNG
Asali: Twitter

Yadda hukumar kwastam ta kama makamai a buhunan shinkafa

Mukaddashin kwanturolan kwastam na yankin Ogun Area 1, Mataimakin Kwanturola Amadu Shuaibu, ne ya bayyana hakan yayin hira da manema labarai a iyakar Idiroko a ranar Talata, 28 ga watan Nuwamba.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Shuaibu ya ce kimanin mako guda kenan hukumar na bibiyar masu shigo da makaman har sai ranar Litinin da misalin karfe 5:00 na asuba lokacin da suka samu bayan sirri na makaman da aka nade a buhunan shinkafa biyar sannan aka boye su a jejin.

Ya ce:

"A yayin binciken, an gano harsasai kimanin guda 975 da aka boye a cikin buhunan."
“Mun kara zage damtse don gano wadanda suka aikata wannan danyen aiki domin gurfanar da su a gaban kuliya.

Shu’aibu ya ce illar fasa-kwaurin makamai da alburusai da ba a kula da su ba yana da muni, kama daga karfafa kungiyoyin masu aikata laifuka zuwa ga barkewar rikici da kuma yin kutse a harkokin tsaron kasa.

Kara karanta wannan

Rigima ta ɓalle, Mataimaki Shaibu ya ɗara caccakar Gwamnan PDP kan zaben jihar na 2024

An tilastawa barayi kwankwadar barasa

A wani labari na daban, mun ji cewa wani bidiyo da ya yadu a ranar Laraba, ya nuno lokacin da aka tilastawa wasu barayi shan barasa da suka sata a wani babban kanti da ke kasar Afrika ta Kudu.

Wani dan jarida a Afrika ta Kudu, Velani Ludidi ne ya wallafa bidiyon, inda ya bayyana cewa barayin sun fasa kantin sannan suka saci giya.

Asali: Legit.ng

Online view pixel