"Ki Je Ki Siya Fili": Yar Najeriya Tsinci N1.5m Cikin Kayan Gwanjo, Mutane Sun Yi Martani

"Ki Je Ki Siya Fili": Yar Najeriya Tsinci N1.5m Cikin Kayan Gwanjo, Mutane Sun Yi Martani

  • Wata ƴar Najeriya kwanan nan ta taki sa'a bayan ta tsinci dala $1850 (N1.5m) a cikin wasu kayan gwanjo da ta siyo domin sayarwa
  • Da abokin ɗan uwanta ya ba ta shawarar ta mayar da kuɗin, sai ta yi sauri ta hana shi tuntuɓar ta a dandalin WhatsApp
  • Mutane da dama sun bayyana mabanbantan ra'ayoyi inda da yawa suka goyi bayanta yayin da wasu suka dage cewa ta mayar da kuɗin

Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi

Wani ɗan Najeriya ya soki ƙanwar abokinsa da ke sayar da kayan sawa na gwanjo bayan ta yi wata tsintuwa.

Budurwar ta ci karo da wani abin mamaki inda ta tsinci dalar Amurka $1850 (N1.5m) da aka saka a cikin tarin kayan gwanjon da ta siya.

Kara karanta wannan

Gwamnan APC a Arewa ya hana amfani da Hijabi a jiharsa? Gaskiya ta bayyana

Yar Najeriya ta tsinci N1.5m a gwanjo
Yar Najeriya ta taki sa'a bayan ta tsinci N1.5m a cikin kayan gwanjo Hoto: Jorge Fernández / Getty Images. (Hoton an yi amfani da shi ne kawai domin misali)
Asali: Getty Images

Da take neman shawara, budurwar ta tuntubi mai amfani da sunan @UncleCCA, a Twitter, wanda ya shawarce ta da ta mayar da kuɗin domin nuna imanin da take da shi.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Da yake ƙarfafa mata gwiwa ta yi abin da ya dace, ya jaddada muhimmancin gaskiya da riƙon amana.

Me budurwar ta yi masa bayan ya ba ta shawara?

Sai dai, bayan bayar da wannan nasihar, mutumin ya lura cewa ba zai iya kallon 'WhatsApp status' ɗin ta ba ko kuma ya tura mata da saƙo.

Ya rubuta:

"Ƙanwar abokina da ke siyar da gwanjo, ta tsinci $1850 a cikin kayan gwanjon da ta saya. Na ce ta mayar da kuɗin ga mai su. A matsayinki na mai imani ki mayar da kuɗin. Yanzu ba na iya ganin 'WhatsApp status' ɗin ta kuma idan na tura mata saƙo ba ya zuwa. Wai me nene ya faru?

Kara karanta wannan

Rikicin Rivers: Gwamna Fubara ya sake kalubalantar Nyesom Wike

Masu amfani da yanar gizo sun mayar da martani

Tambayar da mutumin ya yi ta haifar da ɗimbin martani na barkwanci daga masu amfani da yanar gizo.

@ubig1 ya rubuta:

“Abin takaici, ta kulle ka. Neman ta da ta mayar da kusan miliyan biyu. Na tabbata za ta kalli abun a matsayin abin al’ajabi.”

@Iphie__ yayi ya rubuta:

"Ta hanyar ikon mallaka, kuɗin na ta ne yanzu. Idan ka sayi fili a hannun mutum kuma bai san cewa akwai zinare a filin ba. Da zarar kuɗi da takardun mallaka sun canza hannu, ba zai iya dawowa ya ce zinaren na sa ne ba. Hakan zai iya yin aiki idan an bayar da filin a matsayin kyauta."

@RaybanJohn ya rubuta:

"Idan na mayar da kuɗin sai na san dalilin da ya sa na yi hakan."

@Advantage_EG ya rubuta:

"A ina za ta mayar da kuɗin?"

@Nero365 ya rubuta:

Kara karanta wannan

Wasu manyan jiga-jigan NNPP sun shiga sabuwar matsala bayan hukuncin tsige Abba Gida-Gida

"Idan da ni ne ita, zan cinye kuɗin kuma babu abin da zai faru."

Dan Najeriya Mai Jinya Na Samun N6.1m Duk Wata

A wani labarin kuma, kun ji cewa wani ɗan Najeriya ya bayyana maƙudan kuɗaɗen da yake samu a ƙasar Birtaniya saboda aikin jinyar da ya ke yi.

Ɗan Najeriyan wanda ke aikin jinyar wani tsoho, ya bayyana cewa yana samun albashin N204k duk kwanan duniya, yayin da ya ke samun N6.1m duk wata.

Asali: Legit.ng

Online view pixel