Subhanallahi: Rayukan Mutum 25 Sun Salwanta a Wani Mummunan Hatsarin Mota

Subhanallahi: Rayukan Mutum 25 Sun Salwanta a Wani Mummunan Hatsarin Mota

  • An samu asarar rayuka a wani mummunan hatsarin mota da ya auku a jihar Kwara wanda ya ritsa da motoci uku
  • Hatsarin motar ya yi sanadiyyar rasuwar mutum 25 yayin da wasu mutum 15 suka samu raunuka
  • Hukumar kiyaye gobara ta jihar wacce take ɗauki wajen da hatsarin ya auku ta ce biyu daga cikin motocin sun ƙone

Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi

Jihar Kwara - Aƙalla mutum 25 ne suka rasa rayukansu a wani hatsarin mota da ya auku a ƙauyen Peke da ke kan titin Oko-Olowo- Bode-Saadu a ƙaramar hukumar Moro ta jihar Kwara.

Leadership ta tattaro cewa mutum 15 kuma sun samu raunuka daban-daban a gobarar da ta tashi bayan da wata tankar man fetur da wata babbar motar ɗaukar kaya suka yi karo.

Kara karanta wannan

Innalillahi: Rayukan mutum 11 sun salwanta, wasu mutum 54 sun jikkata a wani mummunan hatsarin mota

Mutum 25 sun rasu a hatsarin mota a Kwara
Hatsarin mota ya salwantar da rayukan mutum 25 a Kwara Hoto: @FRSCNigeria
Asali: UGC

Gobarar ta kuma shafi wata motar bas mai ɗaukar mutane 18 da ke tafiya a kan titin, rahoton The Nation ya tabbatar.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Yadda mummunan hatsarin ya auku

Gobarar ta auku ne a lokacin da wata tankar man fetur mai lamba JJN 17 XW da wata motar bas mai ɗauke da mutum 18 suka yi karo da misalin ƙarfe 3:18 na yammacin ranar Talata a ƙauyen Peke da ke kan titin Ilorin- Bode Saadu.

Kakakin hukumar kashe gobara ta jihar Kwara, Hakeem Adekunle, ya tabbatar da aukuwar lamarin, a wata sanarwa da ya fitar ranar Laraba.

Ya ce tankar man fetur ɗin da ta taso daga jihar Neja ta na amfani da hanyar da ba ta dace ba, wanda hakan ya sa suka yi karo da wata babbar mota wacce ta taho daga jihar Legas.

Kara karanta wannan

Yan bindiga sun rutsa manoma a gonakinsu, sun yi ajalin mutum biyu har lahira a jihar Taraba

Wani ɓangare na sanarwar na cewa:

"Hatsarin ya haifar da gobara da ta cinye motocin biyu cikin sauri, wanda kuma ya shafi motar bas mai ɗauke da mutum 18 wacce ta taho daga Legas."
"A ranar 28 ga watan Nuwamban 2023 sa misalin ƙarfe 5:18 na yamma, hukumar kashe gobara ta jihar Kwara ta kai ɗauki kan wata gobara a ƙauyen Peke da ke kan babban titin hanyar Oko-Olowo-Bode Saadu a ƙaramar hukumar Moro."
"Hatsarin ya ritsa da motar tankar man fetur mai lamba JJN 17 XW, wata babbar motar ɗaukar kaya da motar bas mai ɗaukar mutum 18."

Mutum 11 Sun Halaka a Hatsarin Mota

A wani labarin kuma, kun ji cewa rayukan mutum 11 sun salwanta a wani hatsarin mota da ya auku a jihar Kebbi.

Mutum 54 kuma sun samu munanan raunuka a hatsarin motar wanda ya ritsa da wata motar tirela mai ɗauke da kayayyaki fasinjoji.

Asali: Legit.ng

Online view pixel