Innalillahi: Rayukan Mutum 11 Sun Salwanta, Wasu Mutum 54 Sun Jikkata a Wani Mummunan Hatsarin Mota

Innalillahi: Rayukan Mutum 11 Sun Salwanta, Wasu Mutum 54 Sun Jikkata a Wani Mummunan Hatsarin Mota

  • An samu aukuwar wani mummunan hatsarin mota a jihar Kebbi wanda ya salwantar da rayukan mutum 11
  • Hatsarin motar wanda ya ritsa da wata motar tirela mai ɗauke da kayayyaki da fasinjoji ya kuma yi sanadiyyar jikkata mutum 54
  • Rundunar ƴan sandan jihar Kebbi wacce ta tabbatar da aukuwar lamarin ta bayyana cewa mutanen da suka jikkata ana duba lafiyarsu a asibiti

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi

Jihar Kebbi - Mutum 11 ne suka rasa rayukansu a wani mummunan hatsarin mota da ya auku a hanyar Maiyama/Koko a jihar Kebbi.

Jaridar Channels tv ta ce rundunar ƴan sandan jihar Kebbi ce ta bayyana hakan a ranar Talata, 28 ga watan Nuwamba.

Kara karanta wannan

Yan bindiga sun rutsa manoma a gonakinsu, sun yi ajalin mutum biyu har lahira a jihar Taraba

Mutum 11 sun mutu a hatsarin mota a Kebbi
Mummunan hatsarin mota ya salwantar da rayukan mutum 11 a Kebbi Hoto: @FRSCNigeria
Asali: UGC

Hatsarin wanda ya auku a ranar Litinin ya ritsa da Tirelar DAF mai lamba SKK837X wacce wani direban da har yanzu ba a tantance ko waye ba ya ke tuƙa wa.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Cikin wata sanarwa da kakakin rundunar ƴan sandan jihar Kebbi, Nafiu Abubakar ya fitar, ya ce a cikin motar akwai fasinjoji 65, dukkansu maza waɗanda suka fito daga jihar Sokoto.

Bayan fasinjojin, tirelar na kuma ɗauke da buhunan albasa da buhunan wake da babura shida, inda ta taso daga ƙaramar hukumar Goronyo ta Sokoto zuwa Nijar, rahoton Ripples Nigeria ya tabbatar.

Yadda hatsarin motar ya auku

Wani ɓanngare na sanarwar na cewa:

"A yayin da direban ya isa wani wuri kusa da ƙauyen Dada, ƙaramar hukumar Koko/Besse, motar ta ƙwace masa yayin da kwatsam kan motar ya rabu da jikinta."

Kara karanta wannan

Tashin hankali yayin da rikicin manoma da makiyaya ya barke a jihar Arewa

"Saboda haka, kan motar shi kaɗai sai ya yi cikin daji. Sakamakon haka, fasinjoji 65, dukkansu maza daga jihar Sokoto, ciki har da direban sun samu munanan raunuka daban-daban."

Da samun rahoton aukuwar hatsarin, Abubakar ya ce an aike da tawagar ƴan sandan da ke kula da zirga-zirgar ababen hawa daga sashin Koko zuwa wurin da lamarin ya auku inda suka kai waɗanda abin ya rutsa da su zuwa babban asibitin Koko.

Ya ce yayin da aka tabbatar da mutuwar mutum 11, sauran waɗanda abin ya shafa suna karɓar magani.

Mutum Takwas Sun Rasu a Hatsarin Mota

A wani labarin kuma, kun ji cewa mutum takwas ne suka riga mu gidan gaskiya a wani mummunan hatsarin mota da ya auku a ƙaramar hukumar Irepodun ta jihar Kwara.

Mummunan hatsarin dai ya auku ne a tsakanin wata motar tirela ƙirar Mack da wata motar bas ƙirar Mitsubishi a Oke Onigbin, kan titin Omu-Aran-Ilorin.

Asali: Legit.ng

Online view pixel