Yan Bindiga Sun Halaka Mutum 7 a Wani Kazamin Hari da Suka Kai a Wasu Kauyuka 2

Yan Bindiga Sun Halaka Mutum 7 a Wani Kazamin Hari da Suka Kai a Wasu Kauyuka 2

  • Wasu miyagun ƴan bindiga sun salwantar da rayukan mutum bakwai a wani hari da suka kai a wasu ƙauyuka biyu na jihar Plateau
  • Miyagun ƴan bindigan sun kai harin a ƙauyukan Pukah da Pinper na ƙaramar hukumar Mangu ta jihar
  • Bayan halaka mutum bakwau ɗin kuma, ƴan bindigan sun yi awon gaba da tumakai da sauran dabbobi a yayin harin

Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi

Jihar Plateau - Wasu ƴan bindiga sun kai hari a wasu ƙauyuka biyu a jihar Plateau, inda suka kashe mutum bakwai.

Rahotanni sun ce waɗanda harin ya ritsa da su sun mutu ne biyo bayan harin da maharan suka kai a ƙauyukan Pukah da Pinper na ƙaramar hukumar Mangu da ke jihar a safiyar ranar Alhamis, 30 ga watan Nuwamba.

Kara karanta wannan

Yan bindiga sun halaka mafarauta 18 a wani kazamin artabu

Yan bindiga sun halaka mutum bakwai a Plateau
Yan bindiga sun kashe mutum bakwai a Plateau a wani sabon hari Hoto: @PoliceNG
Asali: Facebook

An gano cewa yayin da aka kashe maza shida da wata mace ɗaya a ƙauyen Pukah, ƴan bindigan sun yi awon gaba da tumaki da wasu dabbobi a ƙauyen Pinper.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Yadda harin ya auku

Wani mazaunin ƙauyen Pukah mai suna John Mark, ya tabbatar wa da jaridar The Punch kisan gillar a ranar Alhamis.

Mark ya bayyana cewa:

"Al’ummar Pukah da ke ƙaramar hukumar Mangu ta jihar Plateau sun fuskanci mummunan hari daga wasu ƴan bindiga a safiyar yau (Alhamis). Sun kuma kai hari a wani ƙauye a ƙaramar hukumar mai suna Pinper."
"A ƙauyen Pukah, sun kashe mace ɗaya da maza shida. Amma a Pinper, sun sace tumakai da yawa kafin su gudu daga ƙauyukan."

Mark wanda ya yi Allah wadai da harin ya ce an kai rahoto ga jami'an tsaro.

Da aka tuntubi kakakin rundunar soji mai kula da wanzar da zaman lafiya a jihar, Kyaftin Oya James, ya ce zai yi magana kan harin amma bai yi hakan ba har zuwa lokacin kammala haɗa wannan rahoton.

Kara karanta wannan

Yan bindiga sun halaka babban jami'in yan sanda a yayin wata musayar wuta

Ƴan Bindiga Sun Halaka Mafarauta

A wani labarin kuma, kun ji cewa wasu ƴan bindiga sun halaka mafarauta 18 a wani ƙazamin artabu da suka yi bayan sun kai hari a jihar Taraba.

Ƴan binɗigan sun yi ƙoƙarin farmakar garin Bali na jihar, amma sun fuskanci tirjiya daga wajen mafarautan inda a dalilin hakam suka halaka 15 daga cikinsu.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng