"Ba Ladabi": Matashi Ya Dambace da Mahaifinsa Bayan Ya Tarar da Shi Cikin Wani Yanayi da Budurwarsa

"Ba Ladabi": Matashi Ya Dambace da Mahaifinsa Bayan Ya Tarar da Shi Cikin Wani Yanayi da Budurwarsa

  • Wani saurayi ya fusata tare da shiga takaici lokaci guda bayan ya isa gida inda ya tarar da mahaifinsa tare da budurwarsa
  • A cewarsa, mahaifinsa bai taɓa sanar da shi cewa zai zo ba wanda hakan ya sanya ya ƙara zarginsa
  • A cikin wani faifan bidiyo da ya yaɗu, abin da ya fara a matsayin musayar zafafan kalamai ya koma ba hammata iska

Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi

A cikin wani faifan bidiyo da ya yaɗu, wani matashi ya yi faɗa da mahaifinsa bayan ya koma gida ya same shi tare da masoyiyarsa.

Matashi ya yi fada da mahaifinsa
Matashin ya kama mahaifinsa da fada bayan ya tarar da shi da budurwarsa Hoto: @_EricLamarBeatz
Asali: Twitter

Wani mai amfani da X, mai suna Hennessey James, ya sanya bidiyon inda ya rubuta:

"Shin wannan matashin ya cika zaƙe wa kan mahaifinsa da budurwarsa? Ko abin da ya aikata ya yi kaɗan? Ku gaya min abin da kuke tunani."

Kara karanta wannan

Bidiyon yadda wani matashi ya tarwatsa bikin auren tsohuwar budurwarsa ya girgiza intanet

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Bidiyon ya fara da nuna lokacin da matsashin ya shiga gidan bayan ya fahimci cewa mahaifinsa na ciki.

Ya koka da cewa wannan ne karo na uku a cikin mako guda da mahaifinsa zai zo ba tare da ya gaya masa ba.

Mahaifi da dansa sun dambace

Yana shiga sai ya tarar da budurwarsa sanye da gajeren wando tana soya kaji a kicin yayin da mahaifinsa ya sha ruwa a can gefe yana hira da ita.

Daga musayar zazzafan kalamai, matashin yayi faɗa da mahaifinsa. Ya ɗauki bidiyo kan yadda komai ya kasance.

Wane martani ƴan soshiyal midiya suka yi

@_damidaChoco ya rubuta:

"A bayyane, babu wani abu da ke faruwa a tsakanin su har yanzu. Amma ku yarda da ni, mahaifin yana da wasu tsare-tsare kuma ɗan ya sani."
"Budurwar ba ta sani ba, aikinta kawai take yi a matsayin suruka. Game da suturar ta, gidanta ne, al'ada ce ta sanya abin da take ganin ya dace da ita."

Kara karanta wannan

"Ki je ki siya fili": Yar Najeriya ta tsinci N1.5m cikin kayan gwanjo, mutane sun yi martani

@iSamsilver ya rubuta:

"Gaskiya abin rashin mutunci ne zuwa wurin mutane ba tare da saninsu ko izininsu ba. Aa wannan ba zan amince da shi ba. Idan ka yi min shirme sai ka gane aya da zaƙinta."

@MESIGO422 ya rubuta:

"Sam ba daidai ba ne ita ma budurwar ba ta kyauta saboda komai zai iya faruwa. Tana iya fita waje su hole da mahaifin ta dawo gida ta nuna kamar komai bai faru ba."

@Brhoelyfather ya rubuta:

"Ka yi tunanin matar ɗanka ta yi ado da irin wannan shigar. Lallai Amurkawa baƙar fata suna ƙoƙari."

Budurwa Ta Tsinci Dami a Kala

A wani labarin kuma, kun ji cewa wata budurwa ta samu sha tara ta arziƙi daga fara yin soyayya da wani saurayi cikin ɗan ƙaramin lokaci.

Ko sati daya ba su yi da fara soyayyar ba, amma budurwar ta samu maƙudan kuɗaɗe lamarin da ya sa jama'a sakin baki cike da mamaki.

Asali: Legit.ng

Online view pixel