Rukayat Shittu: PDP Ta Sha Kaye Yayin da Kotun Daukaka Kara Ta Tabbatar da Nasarar Yar Takarar APC

Rukayat Shittu: PDP Ta Sha Kaye Yayin da Kotun Daukaka Kara Ta Tabbatar da Nasarar Yar Takarar APC

  • Ɗan takarar jam’iyyar PDP, Magaji Abdullahi, ya sha kaye a hannun Rukayat Motunrayo Shittu ta jam’iyyar APC mai mulki
  • Magaji ya kalubalanci nasarar Shittu, wacce ke wakiltar mazabar Owode/Onire a majalisar dokokin jihar Kwara
  • Kotun ɗaukaka ƙara ta tabbatar da nasarar Shittu bayan ta yi watsi da ƙarar da ɗan takarar na PDP ya shigar

Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi

Jihar Kwara - Kotun ɗaukaka ƙara da ke zamanta a Abuja, ta yi watsi da ƙarar da ɗan takarar jam’iyyar PDP, Magaji Abdullahi ya shigar yana ƙalubalantar nasarar Rukayat Motunrayo Shittu a zaɓen ranar 18 ga Maris a mazabar Owode/Onire a jihar Kwara.

Kotun ɗaukaka ƙara ta yanke hukuncin ne a ranar Talata, 28 ga watan Nuwamban 2023.

Kara karanta wannan

Kotun daukaka kara ta raba gardama kan karar da ke neman tsige gwamnan PDP a Arewa

Kotu ta tabbatar da nasarar yar takarar APC a Kwara
Kotun daukaka kara ta tabbatar da nasarar Rukayat Motunrayo Shittu Hoto: @Rukayatshittu06/Court of Appeal
Asali: UGC

A wata sanarwa da ta wallafa a shafinta na X @Rukayatshittu06, ta ce tun da farko kotun sauraron ƙararrakin zaɓe ta bayar da umarnin sake gudanar da zaɓe a rumfunan zaɓe biyar na mazabar, hukuncin da ta ƙalubalanta a kotun ɗaukaka ƙara.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Ƴar majalisar ta jam’iyyar All Progressives Congress (APC) ta ce a ƙarshe hukuncin kotun ɗaukaka ƙara ya kawo ƙarshen taƙaddamar kuma a yanzu za ta iya mayar da hankali sosai kan harkokin wakilci.

Motunrayo ta yaba da hukuncin kotun

A yayin da take godiya ga ɓangaren shari'a, ta rubuta cewa:

"Yana da kyau a lura cewa, wannan ita ce shari’a ta 5 da na shiga ciki tun bayan fitowa ta a matsayin ƴar takarar jam’iyyar All Progressive Congress a watan Yunin 2022."
"A batun kafin zaɓe, na je babbar kotu, kotun ɗaukaka ƙara da kotun koli, kuma a batun bayan zaɓe na je babbar kotu, a yanzu kotun ɗaukaka ƙara. Wannan ya sanya na fahimci wahalar da ɓangaren shari'a da muke yi a ƙasar nan."

Kara karanta wannan

NNPP ta yi rashin nasara, Kotun daukaka ƙara ta yanke hukunci kan nasarar ɗan majalisar jihar Nasarawa

"Saboda yawan kararraki da girman shari’o’in da ke gaban kotu, alƙalai suna aiki ba tare da gajiyawa ba na tsawon kwanaki 7 a mako, ciki har da ranar Lahadi, daga safe zuwa dare kuma ba zai yiwu a yi aiki cikin irin wannan matsin lamba ba tare da an samu kura-kurai a lokaci-lokaci ba."
"Duk da cewa a gaskiya ɓangaren shari’a na buƙatar ya inganta kamar yadda mutane da yawa ke ba da shawara, amma dole ne na ce ɓangaren shari’a ya cancanci a tausaya musu saboda girman nauyin da ke gabansu da kuma yaba wa sadaukarwar da suke wajen gudanar da ayyukansu."

Kotun Ɗaukaka Ƙara Ta Tabbatar da Nasarar Gwamna Kefas

A wani labarin kuma, kun ji cewa kotun ɗaukaka ƙara ta tabbatar da nasarar Gwamna Agbu Kefas na jam'iyyar PDP a zaɓen gwamnan jihar Taraba.

Kotun ta yi watsi da ƙarar da jam'iyyar NNPP da ɗan takararta Sani Yahaya suka shigar suna ƙalubalantar nasarar Gwamna Kefas.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng