Shugaba Tinubu Ya Isa Majalisa Domin Gabatar da Kasafin Kudi, Bayanai Sun Fito

Shugaba Tinubu Ya Isa Majalisa Domin Gabatar da Kasafin Kudi, Bayanai Sun Fito

  • Shugaban ƙasa Bola Ahmed Tinubu ya isa majalisar tarayya domin gabatar da kasafin kuɗin shekarar 2024
  • Wannan shine karo na farko da Tinubu ya gabatar da kasafin kuɗin a gaban ƴan majalisun tun bayan hawansa mulki a ranar 29 ga watan Mayun 2023
  • Ƴan majalisun sun miƙe tsaye domin tarbar Shugaba Tinubu da mataimakinsa, Kashim Shettima a zauren majalisar

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi

FCT, Abuja - Shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu ya isa harabar majalisar tarayya domin gabatar da kasafin kuɗin shekarar 2024 na naira tiriliyan 27.5.

A baya dai majalisar tarayya ta bayyana cewa Shugaba Tinubu zai gabatar da kasafin kudin shekarar 2024 a wani zama na haɗin gwiwa da ya ƙunshi sanatoci da ƴan majalisar wakilai.

Kara karanta wannan

Dirama Yayin da Wasu Sanatoci Suka Tafka Kuskure a Zaman Gabatar da Kasafin Kuɗin 2024

Shugaba Tinubu ya gabatar da kasafin kudi
Shugaba Tinubu zai gabatar da kasafin kudi a gaban yan majalisu Hoto: Asiwaju Bola Ahmed Tinubu
Asali: Facebook

Kamar yadda jaridar TheCable ta ruwaito, shugaban majalisar dattawa, Godswill Akpabio, kakakin jajalisar wakilai, Tajudeen Abbas da dukkan ƴan majalisun tarayya na majalisun biyu, wadanda ke zaune duk sun miƙe domin tarbar Shugaba Tinubu da mataimakinsa, Kashim Shettima.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Rahotanni sun bayyana cewa Tinubu ya shiga zauren majalisar ne da misalin ƙarfe 11:09 na safiyar Laraba, 29 ga watan Nuwamba.

Channels tv ta ce sauran tawagar Tinubu sun haɗa da shugaban ma’aikatan fadar shugaban kasa, Femi Gbajabiamila, sakataren gwamnatin tarayya, George Akume, ministan babban birnin tarayya Abuja, Nyesom Wike, shugaban jam’iyyar APC na ƙasa, Abdullahi Ganduje da sauransu.

Tinubu ya aike da wasiƙa ga majalisa

Shugaban ƙasa Bola Ahmed Tinubu ya aika da wasiƙa ga majalisar tarayya domin bayyana aniyarsa ta gabatar da kasafin kuɗin shekarar 2024.

Shugaban Majalisar Dattawa, Sanata Godswill Akpabio ne ya karanta wasiƙar shugaban kasa a zaman sanatoci na ranar 28 ga watan Nuwamba.

Kara karanta wannan

Shugaba Tinubu ya aike da muhimman saƙo ga majalisar dattawa kan kasafin kuɗin 2024 da zai gabatar

Tinubu Na Son Ciyo Bashi

A wani labarin kuma, kun ji cewa shugaban ƙasa Bola Ahmed Tinubu ya buƙaci amincewar majalisar dattawa domin ciyo bashin dala biliyan 8.69.

Hakan na ƙunshe ne a cikin wata sanarwa da shugaban majalisar dattawa, Sanata Godswill Akpabio ya karanta a ranar Talata 28 ga watan Nuwamba

Asali: Legit.ng

Online view pixel