'Yan Bindiga Sun Hallaka Mutum 3, Sun Sace Wasu 8 a Jihar Kaduna

'Yan Bindiga Sun Hallaka Mutum 3, Sun Sace Wasu 8 a Jihar Kaduna

  • Ƴan bindiga sun kai sabon harin ta'addanci a ƙaramar hukumar Birnin Gwari ta jihar Kaduna inda suka hallaka bayin Allah
  • Ƴan bindigan sun kashe mutum uku tare da sace wasu mutum takwas a harin da suka kai ƙauyen Unguwan Habuja na ƙaramar hukumar
  • Tsagerun sun kuma salwantar da ran wani mutum ɗaya tare da raunata wani mutum bayan sun farmaki hanyar Birnin Gwari zuwa Kakangi

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi

Jihar Kaduna - Ƴan bindiga a ranar Talata sun kai farmaki a ƙauyen Unguwan Habuja da ke ƙarƙashin gundumar Kakangi da ke ƙaramar Hukumar Birnin Gwari a Jihar Kaduna.

Ƴan bindigan a yayin harin sun hallaka mutum biyu a ƙauyen tare da yin garkuwa da wasu mutum takwas.

Kara karanta wannan

'Yan sanda sun cafke mutum 2 masu safarar makamai ga 'yan bindiga a jihar Kaduna

'Yan bindiga sun kai hari a Kaduna
'Yan bindiga sun hallaka mutane a jihar Kaduna Hoto: @PoliceNG
Asali: Facebook

Yadda lamarin ya auku

Wani mazaunin yankin ya ce ɗaya daga cikin wadanda harin ya rutsa da su wani shugaban ƴan banga ne a gundumar Kakangi, cewar rahoton jaridar Daily Trust.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

A kalamansa:

"An kai hari ranar Talata a Kakangi, an kashe mutum biyu tare da yin garkuwa da mutum takwas. Mutanen biyu da aka kashe sun haɗa da shugaban ƴan banga na gundumar Kakangi."
"Kisan ya faru ne a ƙauyen Unguwan Habuja mai tazarar kilomita uku daga garin Kakangi."

Hakazalika, ƴan bindiga sun kashe mutum ɗaya a Gonan Alhaji Muntari daura da hanyar Birnin-Gwari zuwa Kakangi a ranar Litinin, tare da harbin wani mutum wanda yanzu yake karɓar magani a babban asibitin Jibril Mai Gwari da ke cikin garin Birnin Gwari.

Me hukumomi suka ce kan harin?

Ɗan majalisar da ke wakiltar mazaɓar Kakangi a majalisar dokokin jihar Kaduna Yahaya Musa Dan Salio ya tabbatar da faruwar lamarin, inda ya ce an kashe mutane uku a cikin ƙauyukan biyu yayin da aka yi garkuwa da mutum takwas.

Kara karanta wannan

'Yan bindiga sun hallaka Farfesa tare da sace mutum 2 a wani sabon hari

Hakazalika, tsohon shugaban ƙungiyar cigaban masarautar Birnin Gwari (BEPU), Ishaq Usman Kasai, ya tabbatar da harin da aka kai a yankin amma bai yi ƙarin bayani ba.

Ƙoƙarin jin ta bakin kakakin rundunar ƴan sandan jihar Kaduna, Mansur Hassan, ya ci tura domin bai ɗauki kiran wayar da aka yi masa ba, kuma bai dawo da amsar saƙon da aka tura masa ta waya ba.

Ƴan bindiga sun kai hari

A wani labarin kuma, kun ji cewa aƙalla mutum 23 ne suka rasa ransu yayin da wasu ƴan bindiga suka kai farmaki kauyen Anguwan Danko a jihar Kaduna.

Ƴan bindigan masu yawa ne dai suka kai farmaki a ƙauyen cikin tsakar dare tare da cin karensu babu babbaka ta hanyar buɗe wuta kan mai uwa da wabi.

Asali: Legit.ng

Online view pixel