Zaben Ondo: Jigon APC Ya Hango Rashin Nasara Ga Jam'iyya, Ya Bayyana Dalili

Zaben Ondo: Jigon APC Ya Hango Rashin Nasara Ga Jam'iyya, Ya Bayyana Dalili

  • Wasu jiga-jigan jam’iyyar APC na jihar Ondo sun fara fargabar jam'iyyar na iya samun matsala a lokacin zaɓen gwamnan jihar na watan Nuwamba
  • Ɗaya daga cikin ƴaƴan jam’iyyar, Bamidele Oloyeloogun, na ganin cewa zaɓen fidda gwanin da APC ta yi akwai maguɗi, kuma hakan zai sanya ta yi rashin nasara
  • Oloyeloogun ya yi nuni da cewa fusatattun ƴan jam’iyyar APC da ba su ji daɗi ba, za su iya juyawa jam’iyyar baya a lokacin zaɓen watan Nuwamba

Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi

Jihar Ondo - Wani jigo a jam’iyyar APC, Bamidele Oloyeloogun, ya bayyana damuwarsa kan cewa jam’iyya za ta iya yin rashin nasara a zaɓen gwamnan jihar mai zuwa.

Bamidele Oloyeloogun ya yi nuni da da cewa APC ka iya yin rashin nasarar ne idan ba a soke zaɓen fidda gwani na gwamna da ta yi ba a jihar.

Kara karanta wannan

Daga karshe Ganduje ya bayyana wadanda suka kitsa dakatar da shi daga jam'iyyar APC

Jigon APC ya hango rashin nasara a zaben gwamnan Ondo
Wasu daga cikin 'yan takarar zaben fidda gwanin APC na gwamnan Ondo Hoto: Jimoh Ibrahim CFR, OFR, Hon Lucky Orimisan
Asali: Facebook

Zaben APC ya bar baya da kura

Tsohon kakakin na majalisar dokokin jihar Ondo, ya bayyana hakan ne a wani taron manema labarai a Akure a ranar Talata, 23 ga watan Afrilu, cewar rahoton jaridar Vanguard.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Oloyeloogun ya bayyana yadda aka gudanar da zaɓen fidda gwanin a matsayin zamba ga jam’iyyar da mambobinta a jihar.

A cewarsa, idan har ba a soke zaɓen fidda gwanin na jam’iyyar APC ba, jam’iyyar za ta sha kaye a zaɓen gwamnan jihar da za a yi a ranar 16 ga watan Nuwamba.

Ya kuma yi kira ga Shugaba Bola Tinubu da ya sa baki shugabannin jam'iyyar su soke zaɓen fidda gwanin, rahoton jaridar The Eagle ya tabbatar.

Meyasa APC za ta fadi zaben Ondo?

"A matsayina na jigo a jam'iyyar APC a jihar Ondo, ina so in yi gargaɗin cewa idan ba a soke zaɓen fidda gwani na ranar 20 ga watan Afrilu ba, APC za ta yi rashin nasara a zaɓen gwamna na ranar 16 ga watan Nuwamba."

Kara karanta wannan

Ondo 2024: Wanene zai lashe zaben fidda gwanin kujerar gwamna a jam'iyyar PDP?

"A bayyana yake cewa a cikin mazaɓu 202 na jihar babu inda aka gudanar da zaɓe, kawai sun ƙirƙiro lambobi ne."
"Hujjar ita ce, yau mambobin mu ba su yin murna saboda hanyar da aka bi wajen bayyana wanda ya lashe zaɓen ba sahihiya ba ce."
"Yau a jihar Ondo, mambobin jam'iyyar APC sun ɓoye fushinsu a zuciya kuma za du bayyana shi a lokacin zaɓen gwamna na ranar 16 ga watan Nuwamba, duk kuwa da irin barazanar da za a yi musu."

- Bamidele Oloye Oloyeloogun

An lakaɗawa kwamishina duka

A wani labarin kuma, kun ji cewa wasu ƴaƴan jam'iyyar APC sun lakaɗawa kwamishinan lafiya na jihar Ondo, Banj Ajayi, dukan tsiya.

Kwamishinan ya sha duka ne bayan an zarge shi da ɓoye takardar sakamakon zaɓen fidda gwanin gwamna na APC a mazaɓarsa.

Asali: Legit.ng

Online view pixel