An Cafko Fursunoni 10 Cikin Wadanda Suka Tsere a Neja, Ana Ci Gaba da Neman Sauran

An Cafko Fursunoni 10 Cikin Wadanda Suka Tsere a Neja, Ana Ci Gaba da Neman Sauran

  • Hukumar kula da gidajen gyaran hali ta Najeriya (NCOs) ta tabbatar da tserewar fursunoni 109 daga gidan gyaran hali na Suleja a jihar Neja
  • Hukumar ta kuma tabbatar da cafko mutum 10 daga cikinsu tare da taimakon sauran hukumomin tsaro da suka bazama nemansu
  • Fursunonin dai sun arce daga gidan gyaran halin ne sakamakon wani ruwan sama da aka yi wanda ya jawo rugujewar katangar gidan

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi

Jihar Neja - Hukumar kula da gidajen gyaran hali ta Najeriya (NCoS) ta tabbatar da tserewar fursunoni 119 daga gidan gyaran hali da ke Suleja a jihar Neja.

Fursunonin sun tsere ne biyo bayan wani ruwan sama kamar da bakin ƙwarya da ya lalata wasu sassan katangar gidan gyaran halin a daren ranar Laraba.

Kara karanta wannan

Fursunoni 118 sun tsere daga gidan gyaran hali a jihar Neja, an samu bayanai

Fursunoni sun arce a Neja
An cafko fursononi 10 da suka tsere a gidan gyaran hali a jihar Neja
Asali: UGC

Sai dai, hukumar NCoS, ta ce ba ta yi ƙasa a gwiwa ba wajen fara neman waɗanda suka tsere, inda tare da haɗin gwiwar sauran hukumomin tsaro an cafko mutum 10 da suka arce, cewar rahoton jaridar Leadership.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Ta kuma bayyana cewa tana ci gaba da bin diddigin sauran fursononi 109 da suka tsere domin dawo da su zuwa gidan gyaran halin.

Me NCOs ta ce kan lamarin?

Hakan na ƙunshe ne dai a cikin wata sanarwa da mai magana da yawun hukumar NCoS reshen birnin tarayya Abuja, DSC A.S. Duza, ya fitar a safiyar ranar Alhamis, rahoton jaridar Daily Trust ya tabbatar.

"Wani mamakon ruwan sama da ya ɗauki tsawon sa'o'i a daren ranar Laraba, 24 ga watan Afrilu, 2024, ya yi ɓarna a gidan gyaran hali na Suleja da wasu gine-ginen da ke kewayensa."

Kara karanta wannan

Hukumar KADIRS ta garkame rassan babban bankin 6 a jihar Kaduna

"Ruwan saman ya lalata wani ɓangare na gidan gyaran halin, ciki har da katangar da ke kewaye da shi wanda hakan ya bada damar tserewar jimillar fursunoni 119."
"Nan take hukumar ta bazama neman waɗanda suka arce, wanda tare da haɗin gwiwar sauran hukumomin tsaro kawo yanzu an cafko fursunoni 10 da suka tsere tare da tsare su, yayin da muke ci gaba da neman sauran."

- A.S Duza

Fursunoni sun arce a Neja

A wani labarin kuma, kun ji cewa wasu fursunoni sun ranta ana kare a gidan gyaran hali da ke Suleja a jihar Neja bayan an tafka ruwan sama kamar da bakin ƙwarya.

Ruwan saman da aka yi ya jawo wasu sassan gine-ginen gidan gyaran halin sun lalace ciki har da katangar wacce ta ruguje, wanda hakan ya ba fursunonin damar guduwa.

Asali: Legit.ng

Online view pixel