Masu Kantin da Ya Hana 'Yan Najeriya Sayayya Sun Amsa Gayyatar Hukumar FCCPC

Masu Kantin da Ya Hana 'Yan Najeriya Sayayya Sun Amsa Gayyatar Hukumar FCCPC

  • Wani babban kantin sayar da kayyakaki na ƴan ƙasar Sin da ke Abuja ya fuskanci suka a yanar gizo bisa zargin hana ƴan Najeriya shiga
  • A ranar Laraba, 24 ga Afrilu, jami’an hukumar FCCPC sun yi wa masu babban kantin tambayoyi kan zargin nuna wariya ga ƴan Najeriya
  • Jami’an hukumar ta FCCPC sun kai ziyara babban kantin yayin da ake ci gaba da gudanar da bincike kan lamarin a birnin tarayya a Abuja

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi

FCT, Abuja - Masu babban kantin ƴan ƙasar Sin da ke Abuja waɗanda ke fuskantar zargin nuna wariya sun amsa gayyatar hukumar FCCPC a ranar Laraba, 24 ga watan Afrilu.

Hukumar FCCPC ta sanar da hakan a shafinta na X (wanda a baya aka fi sani da Twitter).

Kara karanta wannan

'Yan sanda sun cafke mutum 2 masu safarar makamai ga 'yan bindiga a jihar Kaduna

Jami'an FCCPC sun gana da masu kantin Abujs
Jami'an FCCPC sun kai ziyara kantin da ya hana 'yan Najeriya shiga Hoto: @fccpcnigeria
Asali: Twitter

Babban kantin mai suna Royal Choice, yana sayar da abinci da abubuwan sha irin na ƙasar Sin.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

An nunawa ƴan Najeriya wariya a kanti

A wani faifan bidiyo da aka yi a ranar 21 ga watan Afrilu, wani mazaunin Abuja ya bada labarin yadda aka gaya masa cewa babban kanti ya haramta wa ƴan Najeriya shiga cikinsa.

A ƙarshen mako, mutane da yawa sun nuna rashin gamsuwa game da wannan tsarin da kantin ya zo da shi na sayar da kayayyaki kawai ga ƴan ƙasar Sin.

Hakan ya sanya jami'an hukumar kare hakkin masu siyan kayayyaki da abokan hulɗa ta ƙasa (FCCPC) suka ziyarci kantin.

Hukumar FCCPC ta rubuta a shafin X (Twitter) cewa:

"Karin bayani: Masu babban kanti na Abuja da ke fuskantar zargin nuna wariya sun amsa gayyatar da muka yi musu a yau domin amsa tambayoyi kan zarge-zargen. Jami'an FCCPC sun gudanar da bincike a kantin."

Kara karanta wannan

Abin tashin hankali: Wata 'yar gudun hijira ta yanke jiki, sai dai aka dauki gawarta

"Za mu ci gaba da bada ƙarin bayani yayin da ake ci gaba da gudanar da bincike."

An sake buɗe babban kantin

A halin da ake ciki, da yake bayar da ƙarin bayani, mataimakin manajan kantin, Sanusi Shuaibu, a wata tattaunawa da jaridar The Punch ya bayyana cewa an shawo kan lamarin, kuma jami’an hukumar sun buɗe kantin.

"Eh, mun je hukumar a yau kuma an shawo kan dukkan matsalolin. Ita ma mai babban kanti ta halarci taron da jami’an. Ta yi ƙoƙari ta bayyana halin da ake ciki kuma sun bari duk wanda ke da hannu ya bayyana ainihin abin da ya faru.
"Sun kuma nemi da mu gabatar da wasu takardu wanda mun yi hakan, sun yi wa mai kantin wasu tambayoyi, bayan an kammala taron ne muka bar hukumar sannan suka zo suka buɗe babban kantin"

- Sanusi Shuaibu

Dalilin tsige shugaban hukumar FCCPC

A wani labarin kuma, kun ji cewa shugaban ƙasa, Bola Ahmed Tinubu ya bayyana dalilin da ya sa aka tsige Babatunde Irukere a matsayin shugaban hukumar FCCPC.

Mai girma Shugaba Bola Tinubu ya ce an cire Babatunde Irukere ne saboda rashin iya gudanar da ayyukan ofishinsa yadda ya kamata.

Asali: Legit.ng

Online view pixel