Gaskiyar Zance Kan Batun Gwamnatin Tarayya Za Ta Fara Biyan Albashin Ma'aikatan Jihohi

Gaskiyar Zance Kan Batun Gwamnatin Tarayya Za Ta Fara Biyan Albashin Ma'aikatan Jihohi

  • Gwamnatin tarayya ƙarƙashin jagorancin Bola Tinubu ba ta bayyana shirin karɓar biyan albashin ma’aikatan jihohi da ƙananan hukumomi a Najeriya ba
  • Wannan iƙirarin dai wani mai amfani da shafin X ne ya yi, sannan an kwafe shi an sanya a shafukan Facebook da Instagram, inda ya samo ne daga NAN
  • Sai dai, binciken da aka yi ya nuna cewa ba daga NAN ya ke ba, sannan ba wata sahihiyar kafar watsa labarai da ta kawo rahoto kan lamarin amma an samu wani rubutu na faɗar ra'ayi yana bada shawarar a yi hakan

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi

FCT, Abuja - Maganar cewa gwamnatin tarayya ƙarƙashin jagorancin Bola Tinubu ta shirya daukar nauyin biyan albashin ma’aikatan kananan hukumomi a fadin ƙasar nan ba gaskiya ba ne.

Kara karanta wannan

Daga karshe Ganduje ya bayyana wadanda suka kitsa dakatar da shi daga jam'iyyar APC

Wani mai amfani da X mai suna @Gen_Buhar ya yi iƙirarin cewa gwamnatin tarayya na shirin karɓar biyan albashin ma'aikata a matakin ƙananan hukumomi da jiha.

Gwamnatin tarayya ba ta biyan albashin ma'aikatan jihohi
Gwamnatin tarayya ba ta shirin fara biyan albashin ma'aikatan jihohi Hoto: @DOlusegun
Asali: Twitter

Wani ɓangare na rubutun na cewa:

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

"LABARI DA DUMI-DUMI: Gwamnatin tarayya za ta karɓi biyan albashi daga hannun gwamnonin jihohin ƙasar nan, tare da sauya sunayen ma’aikatan Najeriya. Ya kamata duka ƙananan hukumomi da gwamnatin tarayya su riƙa amfani da IPPIS."

Gwamnatin tarayya ba ta biyan albashi

@Gen_Buhar ya ci gaba da iƙirarin cewa rahoton ya fito ne daga kamfanin dillancin labarai na Najeriya (NAN).

Rubutun, wanda ya sanya aka bayyana mabambantan ra'ayoyi da martani a manhajar X, an kwafe shi kuma an buga a Facebook da Instagram.

Da aka yi amfani da kalmar "Gwamnatin tarayya za ta karɓe biyan albashin ma'aikatan gwamnatocin jihohi" a kan Google, ba a samu wani rahoton a NAN ba ko wasu kafafen yaɗa labarai masu inganci.

Kara karanta wannan

JAMB: Gwamnatin Tinubu ta faɗi mafi ƙarancin shekarun shiga Jami'a a Najeriya

Sai dai, binciken da aka ƙara ya bayyana wani rubutun faɗar ra'ayi da aka yi a shafin The Spectacle, wani shafin yanar gizo da ya wallafa labarin a ranar 22 ga watan Maris, 2024.

Wace shawara aka ba gwamnatin tarayya?

Rubutun faɗar ra'ayin ya yi kira ga gwamnatin tarayya ta samar da albashin bai ɗaya wanda zai kawar da amfani da sunan ma'aikatan jihohi da ƙananan hukumomi tare sa bada shawarar yin amfani da sabon sunan "ma'aikatan Najeriya"

Mai rubutun ya bada shawarar ya kamata gwamnatin tarayya ta riƙa biyan albashin ma'aikata a matakin jiha da na ƙananan hukumomi. Ya yi nuni da cewa hakan zai sanya a samu kuɗaɗen da za a yi wasu ayyukan ci gaba.

Za a ɗauki sababbin ma'aikata

A wani labarin kuma, kun ji cewa gwamnatin jihar Kuros Riba ta bayyana shirinta na daukar sababbin malamai 6000 sakamakon karancin malaman da ake fama da shi a makarantun jihar.

Stephen Odey, kwamishinan ilimi ne ya bayyana hakan yayin ganawa da manema labarai a ofishinsa da ke Kalaba, babban birnin jihar.

Asali: Legit.ng

Online view pixel