'Yan Sanda Sun Sheke 'Yan Bindiga 8 Tare da Ceto Mutanen da Suka Sace a Bauchi

'Yan Sanda Sun Sheke 'Yan Bindiga 8 Tare da Ceto Mutanen da Suka Sace a Bauchi

  • Rundunar ƴan sandan jihar Bauchi ta tabbatar da samun nasara kan ƴan bindiga da ake zargi da yin garkuwa da mutane domin kuɗin fansa a jihar
  • Jami'an rundunar tare da haɗin gwiwar mafarauta sun yi nasarar hallaka ƴan bindiga mutum takwas tare da ceto mutum uku sa suka yi garkuwa da su
  • Kakakin rundunar ƴan sandan jihar Bauchi, SP Ahmed Wakili, shi ne ya tabbatar da samun nasarar a cikin wata sanarwa da ya fitar

Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi

Jihar Bauchi - Jami’an ƴan sanda tare da haɗin gwiwar mafarauta a jihar Bauchi sun yi nasarar kashe wasu mutum takwas da ake zargin masu garkuwa da mutane ne.

Jami'an ƴan sandan sun samu nasarar ne a wani artabu da suka yi da ƴan bindigan a kan iyakar jihar Bauchi da Filato.

Kara karanta wannan

Zamfara: 'Yan bindiga sun hallaka mutum 3 a wani sabon harin ta'addanci

'Yan sanda sun hallaka 'yan bindiga
'Yan bindiga takwas sun bakunci lahira a Bauchi Hoto: @PoliceNG
Asali: Twitter

A yayin samamen, jami'an rundunar ƴan sandan sun kuma ceto kimanin mutane uku da aka yi garkuwa da su, waɗanda aka sace domin neman kuɗin fansa, cewar rahoton jaridar Leadership.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Kakakin rundunar ƴan sandan jihar Bauchi, SP Ahmed Wakil ne ya bayyana hakan ga manema labarai a Bauchi a ranar Alhamis.

Yadda aka sheƙe ƴan bindigan

Ya bayyana cewa jami'an ƴan sandan sun yi arangama da ƴan bindigan ne lokacin da suke aikin sintiri na yau da kullum, rahoton All News ya tabbatar.

"Jami’an ƴan sanda na Gumau, Tilde, da Tulu, sun ci karo da ƴan bindiga a lokacin da suke sintiri, inda suka buɗe wuta domin kare kansu wanda hakan ya yi sanadiyyar kashe wasu mutum huɗu da ake zargin masu garkuwa da mutane ne."
"Biyu daga cikin wadanda ake zargin lokacin da suke kan gargarar mutuwa sun amsa amsa laifin yin garkuwa da mutane da dama a jihohin Bauchi da Filato, ciki har da kisan gilla da aka yi wa mai unguwar ƙauyen Ruruwai."

Kara karanta wannan

'Yan bindiga sun hallaka mutum 3, sun sace wasu 8 a jihar Kaduna

"A wata arangama da aka yi da sauran ƴan bindigan da ke gadin waɗanda aka yi garkuwa da su, an kashe mutum huɗu sannan an ceto mutum uku da aka sace domin a biya kuɗin fansa."

- SP Ahmed Wakili

Ƴan bindiga sun kai hari a Zamfara

A wani labarin kuma, kun ji cewa ƴan bindiga sun kai sabon harin ta'addanci a garin Zurmi, hedkwatar ƙaramar hukumar Zurmi ta jihar Zamfara

Ƴan bindigan a yayin harin sun hallaka mutum uku tare da yin garkuwa da mutum ɗaya bayan sun lalata ƙarfen sabis na MTN da ke garin.

Asali: Legit.ng

Online view pixel