Zamfara: 'Yan Bindiga Sun Hallaka Mutum 3 a Wani Sabon Harin Ta'addanci

Zamfara: 'Yan Bindiga Sun Hallaka Mutum 3 a Wani Sabon Harin Ta'addanci

  • Wasu miyagun ƴan bindiga ɗauke da makamai sun kai hari a garin Zurmi, hedkwatar ƙaramar hukumar Zurmi ta jihar Zamfara
  • Ƴan bindigan a yayin harin sun hallaka mutum uku tare da lalata ƙarfen sabis na kamfanin MTN da ke garin wanda ya haifar da yankewar sabis a yankin
  • Kakakin rundunar ƴan sandan jihar Zamfara ya tabbatar da aukuwar lamarin inda ya ce jami'an rundunar sun fafata da ƴan bindigan domin daƙile harin

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi

Jihar Zamfara - Wasu ƴan bindiga sun kai hari ƙauyen Dauran da garin Zurmi, hedkwatar ƙaramar hukumar Zurmi ta jihar Zamfara.

Ƴan bindigan a yayin harin sun kashe mutum uku tare da yin garkuwa da wasu mutanen da ba a tantance adadinsu ba.

Kara karanta wannan

'Yan sanda sun sheke 'yan bindiga 8 tare da ceto mutanen da suka sace a Bauchi

'Yan bindiga sun kai hari a Zamfara
'Yan bindiga sun hallaka mutum uku a Zamfara Hoto: @daudalawal
Asali: Twitter

Yadda lamarin ya auku

A yayin harin da ƴan bindigan suka kai ranar Laraba da daddare, sun kuma ƙona ƙarfen samar da sabis na MTN a garin, wanda hakan ya haifar da yankewar sabis a yankin, cewar rahoton tashar Channels tv.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Wani mazaunin garin Nasiru Zurmi ya bayyana cewa ƴan bindigar sun mamaye garin ne da misalin ƙarfe 9:00 na dare bayan sun yi garkuwa da mutum biyar a ƙauyen Dauran.

A cewarsa, an kashe mutum uku a garin Zurmi yayin da aka yi garkuwa da wasu da ba a san adadinsu ba a fadar Sarkin garin.

"Ƴan bindigan sun shigo garin ne da manyan makamai da misalin ƙarfe 9:00 na dare, sun kashe mutum uku tare da yin garkuwa da mutum uku a fadar Sarki, ƴan bindigan sun kuma kai hari Dauran tare da yin garkuwa da mutum biyar."

Kara karanta wannan

'Yan bindiga sun hallaka mutum 3, sun sace wasu 8 a jihar Kaduna

- Nasiru Zurmi

Me ƴan sanda suka ce kan harin?

Ko da Legit Hausa ta tuntuɓi kakakin rundunar ƴan sandan jihar Zamfara, Yazid Abubakar ya tabbatar da faruwar harin.

Ya ce an kashe mutum uku a harin amma ya ce mutum ɗaya ne kawai ƴan bindigan suka sace.

"Eh, an kai hari a garin Zurmi jiya da daddare kuma jami'anmu sun fafata domin daƙile harin, amma abin takaici an kashe mutum uku tare da yin garkuwa da mutum ɗaya.
"An kuma ƙona ƙarfen samar da sabis na MTN da ke aiki a garin yayin harin. Ana ci gaba da ƙoƙarin ganin an kuɓutar da mutumin da suka sace."

- Yazid Abubakar

An farmaki ƴan bindiga a Zamfara

A wani labarin kuma, kun ji cewa dangin wata amarya da ake daf da ɗaura mata aure sun daƙile yunƙurin garkuwa da mutane da ƴan bindiga suka yi a Zamfara.

Lamarin ya faru ne lokacin da ƴan bindiga suka yi wa dangin amaryar da wasu matafiya kwanton ɓauna a titin Talata Mafara zuwa Gusau.

Asali: Legit.ng

Online view pixel