Manyan Labarai A Yau
Wasu almajirai mutum bakwai sun rasa rayukansu bayan rami ya fado musu a jihar Kebbi. Almajiran dai sun je debo kasa ne lokacin da lamarin ya auku.
Kwamoshinan lafiya na jihar Ondo ya sha dukan tsiya bayan an zarge shi da boye takardar sakamakon zaben fidda gwanin gwamna na jam'iyyar APC a mazabarsa.
Shugaban rukuninin kamfanonin Dangote, Aliko Dangote ya ce matatar man fetur ta Dangote ta zaftare farashin man dizal ne domin a samu saukin kayayyaki a kasar nan.
An samu asarar rayuka bayan an gwabza fada a tsakanin 'yan bindiga da 'yan banga a jihar Sokoto. Mutane da dama sun rasa rayukansu a dalilin arangamar.
Mai ba shugaban kasa shawara kan harkokin tsaro, Malam Nuhu Ribadu ya bayyana dalilan da suka haddasa matsalar rashin tsaron da ake fama da ita a Najeriya.
Hadimin kakakin majalisar dokokin jihar Kogi, ya yi magana kan bukatar da aka yi na majalisar ta tsige Gwamna Ahmed Usman Ododo, kan zargin ya taimaki Yahaya Bello.
Rundunar 'yan sandan Najeriya ta dauki mataki kan jami'anta da ke tare da tsohon gwamnan jihar Kogi Yahaya bisa zargin sun taimaka masa ya tsere daga kamu.
Wasu miyagun 'yan bindiga sun aikata ta'asa a kan titin Kakangi zuwa Birnin Gwari. Tantiran sun hallaka jami'an tsaro na 'yan banga mutum 3 tare da sace 'yan kasuwa.
Kwamishinan yada labarai na jihar Kogi, Kingsley Fanwo, ya fito ya yi magana kan dambarwar da ta faru yayin da hukumar EFCC ta yi kokarin cafke Yahaya Bello.
Manyan Labarai A Yau
Samu kari